Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na son Osimhen, Barca na shirin biyan kuɗin Dani Olmo
Brighton ta tuntuɓi tsohon ɗanwasan baya na Bayern Munich da Borussia Dortmund Mats Hummels, mai shekara 35, wanda ya lashe Kofin Duniya da Jamus a 2014, kodayake za su iya fukantar hamayayya daga West Ham. (Sky Sports)
Manchester United na shirin taya ɗanwasan Burnley da Norway Sander Berge, mai shekra 26, bayan Old Trafford ta haƙura danwasan Paris St-Germain mai shekara 23 ɗan ƙasar Uruguayan Manuel Ugarte. (Athletic - subscription required)
Sai dai Burnley za ta nemi a biya ta kusan fam miliyan 30 kan ɗanwasan tsakiyar. (Sun)
Arsenal na cikin ƙungiyoyin da ke sha’awar ɗanwasan gaba na Najeriya da Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25, duk da Paris St-Germain na son ɗanwasan. (Gianluca di Marzio on X)
Barcelona ta cimma matsaya ta fatar baki kan fam miliyan 47.3 kan ɗanwasan gaba na RB Leipzig Dani Olmo, mai shekara 26. (Fabrizio Romano on X)
Tottenham na son ɗanwasan gaba na Bournemouth Dominic Solanke, zuwansa ya dogara ne da makomar ɗanwasan Brazilian Richarlison. (Standard)
Spurs ta shirya rabuwa da Richarlison inda take jiran tayi daga Saudi Pro League. (Football Insider)
Bayern Munich har yanzu ba ta yanke shawara kan ɗanwasan Bayer Leverkusen da Jamus Jonathan Tah.
Brentford ta taya ɗanwasan baya na Burnley da Jamhuriyyar Ireland Dara O'Shea, mai shekara 25. (HITC)
Ajax, Feyenoord da PSV na hamayya kan ɗanwasan baya na Coventry City mai shekara 23 Milan van Ewijk. (ESPN - in Dutch)
West Ham na jiran tayi kan ɗanwasanta na Ingila mai shekara 32 Danny Ings. (Football Insider), external
Golan Aston Villa James Wright, mai shekara 19, na tattaunawa domin kowama is Real Union, da ke buga wasa a lig din Spain mataki na uku. (Athletic - subscription required)
Atletico Madrid na ci gaba da tattaunawa da Valencia kan ɗanwasan tsakiya mai shekara 21 Javi Guerra. (Athletic - subscription required)
Ɗanwasan baya na Chelsea Alfie Gilchrist, mai shekara 20 ana shirin diba lafiyarsa domin komawa Sheffield United a matsayin aro. (Sky Sports)