Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham ta ɗauki Rodriguez wanda ya taka leda a Real Betis
West Ham United ta kammala ɗaukar ɗan wasan Argentina, Guido Rodriguez, bayan da bai da ƙwantiragi da kowace ƙungiyar.
Ɗan wasan mai shekaru 30, ya koma West Ham ne bayan da yarjejeniyarsa ya kare da Real Betis mai buga La Liga, wanda ya yi kaka hudu da rabi a can.
Rodriguez ya buga wa Argentina wasa 30, wanda yana cikin waɗanda suka lashe kofin duniya a Qatar a 2022 da ɗaukar Copa America biyu.
"Ina jin burin kowane ɗan kwallo ne ya taka leda a gasar Premier, kuma na yi matukar farin ciki da na ji cewa West Ham na sha'awa ta," in ji Rodriguez.
Rodriguez wanda ya fara taka leda a River Plate, ya kara da cewa ya tattauna da ɗan wasan West Ham da Mexico, Edson Alvarez game da komawa gabashin Landan kafin ya amince ya koma Premier.
Rodriguez da Alvarez sun taka leda a baya a Club America ta Mexico.
West Ham ta kashe sama da fam miliyan 100 kawo yanzu a kakar bana, wajen ɗaukar ƴan wasa, tun bayan da ta naɗa sabon koci, Julen Lopetegui.
Tuni kuma da ɗauki Crysencio Summerville daga Leeds United da Niclas Fullkrug daga Dortmund da Luis Guilherme daga Palmeiras da mai tsaron baya Max Kilman daga Wolverhampton.