Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Na fuskanci kalubale zuwa na Chelsea kan fam miliyan 115 - Caicedo
Moises Caicedo, ya ce kakarsa ta farko a Chelsea ta kasance "mai tsauri" kuma ya kasa samun kwarin gwiwa, saboda an saye shi kan farashin fam miliyan 115.
Ɗan wasan tawagar Ecuador, mai shekara 22, ya koma Chelsea daga Brighton a watan Agustan bara kan fam miliyan 100, har da karin tsarabe-tsarabe da ya kai fam miliyan 115.
Ƙungiyar Stamford Bridge ta dauki ɗan wasan a matakin mafi tsada a Burtaniya, bayan da Liverpool ta yi zawarcinsa.
Ya ci ƙwallo daya ya bayar da huɗu aka zura a raga a wasa 48 a kakarsa ta farko a Chelsea, wadda ta kare a mataki na shida a teburin Premier a bara.
Bayan kammala kakar da ta wuce ne Chelsea ta raba gari da koci, Mauricio Pochettino cikin watan Mayu, bayan da suka cimma matsaya a tsakaninsu.
Caicedo ya ce "Farkon kaka a Chelsea na sha ɗan karen wahala, saboda kana babbar ƙungiya, sannan an sayo ka da ɗan karen tsada, ya zama wajibi ake cin wasa da kai.''
''Na sha wahala matuka, domin lokacin da nake Brighton ban fuskanci irin kalubalen ba, kenan na shiga wani yanayi na daban.''
"Amma bayan wata hudu ko zuwa biyar da suka wuce, daga nan ne hankali na ya kwanta, sannan na fara jin daɗin taka leda a ƙungiyar.''
Da aka tambaye shi ko ya rasa kwarin gwiwa ne, Caicedo sai ya ce: "Eh, na rasa kwarin gwiwa. Duk da ina da ƙwarewa, kuma nasan ko ni wanene a fannin taka leda.
Caicedo ya yaba wa tsohon kociyan Chelsea, Pochettino kan yadda ya ja ragamar ƙungiyar a kakar da ta wuce da damar da ya bashi ta nuna kansa.
"Mutane da yawa na kusa da ni sun taimake ni - Mauricio da ma'aikatansa. Suna tare da ni lokacin da nake jin kamar ba nine Moises ba," in ji shi.
"Wani mutum da nake magana da shi akai-akai ya gaya min cewa, 'Moises, kai ɗan wasa ne mai kyau, za ka iya yin duk abin da kake so a filin tamaula.''
''Ka amince da kanka, kuma kasan cewar Chelsea ta ɗauke ka da ƙudi mai tsoka, domin ka dace, kuma fitatcen ɗan ƙwallo ne kai.''
Chelsea ta ɗauki sabon koci, Enzo Maresca a bana, domin ya ja ragamar kungiyar daga Leicester City, bayan da ya lashe Championship a kakar da ta wuce.