Ƴanbinbiga sun sace ɗaliban da ke rubuta NECO a jihar Kogi

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan jihar Kogi ta tabbatar da yin garkuwa da ɗalibai huɗu da ke rubuta jarrabawar NECO da wasu malamai biyu cikin har da shugaban makarantar.
Cikin wata sanarwar kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Salisu Oyiza ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da yamma lokacin da ɗaliban ke tsaka da rubuta jarrabawar NECO a makarantar Sakandiren Edo-Ekina da ke yankin ƙaramar hukumar Dekina.
Ƴansan sun kuma ce sun kai ɗaukin gaggawa tare da ƙaddamar da bincike kan lamarin.
“Tawagar hadin giwar jami'an tsaro sun gaggauta ƙaddamar d aneman ɗaliban, waɗanda har yanzu kuma suna neman jami'an'', in ji sanarwar.
ASP Oyiza ta ce zuwa yanzu jami'an tsaro sun kuɓutar da ɗalibi ɗaya, yayin da suke ci gaba da neman sauran tare da farautar maharan.
Lamarin na zuwa kwanaki bayan kuɓutar da ɗaliban makarantar jihar Oyo da suka kwashe makonni a hannun ƴanbindiga.

















