Ƴan wasan Tottenham suna goyon bayan Postecoglou - Maddison

Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

James Maddison ya ce ƴan wasan Tottenham suna goyon bayan Ange Postecoglou, kuma idan aka ci gaba da bashi dama zai mayar da ƙungiyar kan ganiya.

Tottenham tana ta 16 a kasan teburin Premier na bana, hakan ya sa kociyan ke fuskantar matsi, duk da kokarin da yake a gasar zakarun Turai ta Europa League.

Ƙungiyar da ke Arewacin Landan ta yi shekara 17 rabon ta da lashe kofi, za ta karɓi bakuncin Bodo/Glimt a wasan farko a daf da karse gasar ta zakarun Turai ranar Alhamis.

Maddison, mai shekara 28 ya ce ya ƙwan da sanin suna fuskantar koma baya a kakar nan, amma ya ce matsin da kociyan ke fuskanta bai kamata ba.

''Muna tare da shi ɗari bisa ɗari,'' in ji Maddison. ''Mutum ne na gari. Mun ci karo da kalubale ne kawai, musamman a lik. Amma muna da ƙyau a gasar Turai.''

Tottenham za ta kara da Bodo ba tare da ƙyaftin, Son Heung-min, wanda ke jinya.

Maddison ya kara da cewar suna sa ran kai wa zagayen karshe a karon farko tun bayan rashin nasara a hannun Liverpool a 2019 a Champions League.