An yi wa Rudiger tiyata amma ba a fayyace ranar da zai warke ba

Rudiger

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta sanar ranar Talata da cewar, an yi wa Rudiger tiyata, sakamakon raunin da ya ji a gwiwa.

Dakta Manuel Leyes ne ya yi masa aikin a karkashin kulawar likitan Real Madrid, an kuma sanar cewar an yi aikin cikin nasara.

Sai dai ƙungiyar ta Santiago Bernabeu ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba, balle a san ranar da zai koma fagen fama.

Rudiger ya ce ya daɗe yana ɗauke da raunin, kuma haka yake taka leda cikin radaɗi.

''Ina son na warke da wuri, domin akwai manyan wasannin da ke gaba na da ya haɗa da Nations League da kuma Club World Cup.''

''Amma yanzu ina bukatar yin jinya, zan kuma yi dukkan abin da ya kamata, domin na koma fagen fama da wuri.''

An bai wa Rudiger jan kati a wasa da Barcelona, sakamakon jifan alkalin wasa, saboda ransa ya ɓaci bisa ketar da aka yi wa Kylian Mbappe.

Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar a Santiago Bernabeu.

Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da ɗan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa huɗu zuwa 12.

Real, wadda take ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama, za ta karɓi bakuncin Celta Vigo ranar Lahadi.