Manchester City ta yi nasara kan Wolves a ƙarshen lokaci

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi nasara a wasa mako na takwas a gasar Premeir kan Wolves da ci 2-1 a ƙarshen lokaci.
Wasan wanda City ta buga shi tamkar sauran wasanninta da kyau, ya ba ta wuya ta fuskar zura kwallaye.
A minti na bakwai da fara wasa ɗan wasan Wolves Jorgen Strand Larsen ya jefa kwallo a ragar City.
Sai a minti na 33 da fara wasan Jasko Gvardiol ya farke wasa Manchester City, wanda hakan ke nufin yanzu shi ne ɗan bayan Premier da ya fi cin kwallo a 2024, inda ya ci shida.
An ci gaba da buga wasan City na ta kai ruwa rana domin samun nasara, amma Wolves na iya ƙoƙarinta domin ganin ta tsira da maki ɗayan da suka raba a lokacin.
A minti na 89 alƙalin wasa ya bayar da umarnin ƙara minti biyar a wasa, wanda a cikinsu ne John Stone ya ƙara ta biyu da ka, wadda ta bai wa City nasara a a wasan.
Kwanar da John Stone ya ci ita ce ta 18 da Manchester City ta ci a wannan kakar, da haka kuma ta fi ko wacce ƙungiya yawancin kwana.
A wasan City ta yi fasin tsakanin 'yan wasanta 722 kuma 651 sun ta fi yadda ake so.










