Rashin alƙibilar gwamnatin Trump kan harkokin waje ya sa duniya kame-kame

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Tom Bateman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, State Department Correspondent
- Aiko rahoto daga, Frankfurt
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Tsagewar gilashin jirgin saman da ke ɗauke da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ta sa dole ya juyo daga tafiyar da yake yi zuwa babban taron tsaro da zai halarta a birnin Munich na Jamus.
Babban jami'in diflomasiyyar na Amurka tare da tawagar jami'ansa da 'yanjarida da ke tare da shi a jirgin sun juya ne suka koma Washington, bayan sun shafe sa'a ɗaya suna tafiya a jirgin, a ranar Alhamis.
Duk da wannan fargaba da Sakataren da tawagar tasa ke ciki kan tsagewar gilashin jirgin, tuni labarin ya bazu.
Can a Turai, Sakataren tsaron Amurkar, Pete Hegseth, ya ba ƙawayen Amurkar mamaki tare da sanya su cikin hali na rashin me za su yi bayan jawabin da ya yi da ke nuna cewa dole ne Ukraine ta haƙura da wasu buƙatunta domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha, wadda Shugaba Trump zai shirya.
Hegseth, ya ce ba abu ne mai yuwuwa ba Ukraine ta samu yankunan da Rasha ta ƙwace mata su sake komawa ƙarƙashinta ba, kamar yadda kuma dole ne maƙwabciyar ta Rasha ta haƙura ta maganar shiga ƙungiyar NATO, inda ya ƙara da cewa ya rage da Turai ba sojojin Amurka ba ta tabbatar da zaman lafiyar.
Masu sharhi ciki har da 'yan jam'iyyar Republican a Washington sun yi kakkausar suka ga jawabin na Hegseth, da cewa Amurka ta sallamar da Ukraine ga Rasha tun ma kafin tattaunawar zaman lafiyar.
Tsohon Firaministan Sweden kuma ɗaya daga cikin shugabannin majalisar masana kan harkokin waje ta Turai, Carl Bildt, ya ce, ''wannan wani sabon abu ne ka sallama wasu muhimman muradu tun kafin a fara zaman tattaunawar yarjejeniya.''

Asalin hoton, EPA
Kwana ɗaya bayan wannan kalami na, Hegseth, sai kuma ya sauya baki, inda ya ce, za a iya tattauna komai a zaman sasanton tsakanin Shugaba Putin da Zelensky na Ukraine.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mista Hegseth ya ƙara da cewa abin da ya faɗa da farko, ainahin zahirin abin da su suke gani shi ne gaskiyar lamari game da rikicin na Rasha da Ukraine, yana mai watsi da batun cewa Amurka ta bayar da kai ga Moscow a kan Ukraine.
Shi kuwa Sakataren Wajen Amurka, Rubio, wanda matsalar tsagewar gilashin jirgin samansa ta jinkirta isarsa taron na Munich, jami'ansa da ke birnin na Jamus na bayar da bayani a kan abubuwan da zai ba wa fifiko a taron.
Jami'an na bayani cewa Amurka za ta yi aiki ne domin tabbatar da gaskiya da adalci inda ƙasashen Turai za su shige gaba wajen samar da daftarin zaman lafiya mai ɗorewa, in ji su.
A ranar Litinin ake sa ran shugabannin Turai za su gana a Paris domin tattaunawa ta gaggawa ta neman tabbatar da ganin ƙasashen Turai sun taka rawa sosai a duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi a kan Ukraine.
Matsayar Sakataren Wajen Amurkan ba ta nuna wata alama ta taƙaita hurumin Ukraine ba, kamar yadda takwaransa na tsaro ya yi.
Sannan kuma can a Jamus ɗin ma a birnin na Munich, inda mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya jagoranci tawagar Amurka a taron, ya ce ƙasarsa za ta iya amfani da ƙarfin soji ta tilasta wa Rasha ta amince a yi yarjejeniya, wanda wannan kalami nasa ya saɓa da na Hegseth, wanda ya ce ba sojin Amurka da za a tura Ukraine.
Bayan duka wannan, can kuma a ofishin Trump an tattauna kalaman na jawabin Hegseth - tare da sharhin da wani Sanata na jam'iyyar Republican ya yi, wanda ya bayyana kalaman a matsayin kuskure, wanda tamkar wani mai goyon bayan Shugaba Putin ya rubuta.
Sanatan ya ƙara da cewa da Trump ya san abin da Hegseth zai ce to da ba makawa, ''shugaban ya ce, '' Zan yi magana da Pete, zan bincika.''

Asalin hoton, Reuters
Kwana uku na kwan-gaba-kwan-baya ya nuna matsayar gwamnatin Trump a kan ɗaya daga cikin muhimman batutuwa masu sarƙaƙiya da yake fuskanta - wato yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine - da kuma yadda gwamnatin ke tsarawa da kuma fitar da saƙonninta a kan manufofinta na ƙasar waje.
A kan batun, jawabin Hegseth tare da dogon jawabin da Trump ya yi a kan tattaunawar waya da Trump ya yi da Putin da nufin shirya wata tattaunawar zaman lafiya kan Ukraine, sun tayar da hankalin shugabannin Turai, duk da yunƙurin Hegseth na janye kalaman da ya yi tun da farko.
''Duk wani sasanto na gaggawa ɓara gurbi ne,'' in ji babbar jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai Kaja Kallas - da take martani kan tattaunawar da AAmurka ke neman shiryawa da Rasha, wadda ka iya barin Ukraine a gefe.
Akwai kuma maganar yadda ake bayyana manufofin waje na Amurka a ƙarƙashin gwamnatin Trump.
Abin da ya faru a Munich kusan wani yunƙuri ne na manyan jami'an shugaban na fassarawa tare da bayyana matsayin Trump, to amma wannan yunƙurin a wani lokaci yakan haifar da kalamai masu karo da juna, inda wasu daga cikinsu ake ƙoƙarin yayyafa musu ruwa ko ma a janye su.
Zuwa yanzu ba za a iya cewa ƙarara ba yadda wannan kwan-gaba-kwan-baya ko katoɓara ta gwamnatin ta Trump za ta ci gaba da kasancewa ba dangane da manufofin gwamnatin na waje - musamman ma a kan gwamnatin da shugabancin ƙasar bai damu da irin katoɓarar da jami'anta ke yi ba - duk kuwa da yamutsin da hakan ke haifarwa matuƙar dai jami'an za su ci gaba da zama 'yan-amshin-shatan shugaban.
Wa'adin mulkin farko na Trump ya gamu da matsalar sauka ko korar manyan jami'ai waɗanda kalamansu suka ci karo da nasa ko kuma suka samu saɓani da shi, ciki har da masu bada shawara na ƙasa da sakatarorin tsaro biyu da kuma sakataren waje ɗaya.
A wannan karon naɗe-naɗen da ya yi na nuni da alama ta waɗanda a shirye suke su zama tamkar raƙumi da akala a gare shi.
Pete Hegseth, wanda bai taɓa wani aiki na shugabantar wata hukuma ta soji ko gwamnati ba, tsohon mai gabatar da shirin talabijin ne na tashar Fox News, kuma tsohon jami'in hukumar tsaron shugaban ƙasa ne - mai muƙamin manjo, wanda ra'ayinsa ya zo daidai da na Trump.
An yi adawa da ja sosai wajen amincewa da naɗinsa inda sanatoci uku na Republican suka jefa ƙuri'ar ƙin amincewa da shi, lamarin da ya sa ƙuri'ar ta zama ba rinjaye sai da mataimakin shugaban ƙasa JD Vance ya kaɗa tasa sannan ya tsallake.

Asalin hoton, EPA
Kamar yadda shi kansa Trump ya ce a wannan makon ya yarda da maganar fitar da batun shigar Ukraine NATO daga tattaunawar, yana mai cewa, ''ba abu ne mai yuwuwa ba.''
A taƙaice wannan ya nuna cewa kalaman Hegseth daidai suke da matsayin Trump - illa dai an yayata su ne ga waɗanda suke son ganin ba a mayar da Ukraine baya ba a tattaunawar.
Ƙalubalen da waɗanda wannan abu ya shafa shi ne ainahin matsayin manufofin waje na Amurka waɗanda ke kasancewa tamkar wani abu da ba za a saɓa ba. Ɗaya daga cikin muhimman abubuwanta shi ne rashin tabbas - wannan zai iya kasancewa abu ne da ake yi da sani - wato kenan Donald Trump na amfani da salon manufar nan da ake dangantawa da halayyar mahaukaci - wadda aka san tsohon shugaban Amurka Richard Nixon na Republican da ita.
Wannan na nuna yuwuwar kasancewar matsayin shugaban mai ƙarfin iko amma kuma wanda ba za a iya sanin inda ya nufa ba ballantana a yi hasashen abin da zai yi wata hanya ce ta sa abokanai su kasance kusa da shi yayin da yake takura wa abokan gaba.
To amm kuma kamar yadda wannan nazariyya da ake dangantawa da mahaukaci ta nuna tana tattare da haɗari ko kura-kurai sosai a wannan duniya da ke fama da tashin hankali da kuma rashin tabbas.
Maganar da Trump ya yi kan Gaza - ta kwashe Falasɗinawa zuwa wasu ƙasashe sannan a gina wata sabuwar alƙarya a wajen mallakar Amurka - ita ma ta gamu da ce-ce-ku-ce da ruɗani.
Yayin da wasu jami'ansa suka yi ƙoƙarin yi wa kalaman nasa kwaskwarima cewa kwashe Falasɗinawan abu ne na wucin-gadi kafin a sake gina Zirin - daga baya Trump ɗin ya sake fitowa ya ce abu ne na dindindin - Falasɗinawan ba su da 'yancin komawa.
Yayin da shi Rubio - yake son ma'aikatar harkokin waje ta zama hukumar gwamnati mafi tasiri idan ana magana kan tsare-tsare da manufofin gwamnatin Trump - tuni kalaman abokan aikinsa a Munich suka shafe nasa.
A ƙarshe dai Mista Rubio ya sauka a Munich da wani ƙaramin jirgi ba tare da tsagaggen gilas ba - amma kuma ba tare da tawagar 'yanjarida ba, yayin da tuni wasu ke fitar da labaran da ke ɗaukar hankali -maimakon a ji su daga wajensa.











