Arsenal za ta bada Gyokeres a cinikin Alavarez, Liverpool ta dage kan Barcola

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na nazarin bayar da ɗan wasan gaba na Sweden, Viktor Gyokeres mai shekara 28, a wata yarjejeniya domin sayen ɗan wasan gaba na Argentina na Atletico Madrid, Julian Alvarez mai shekara 26.

Barcelona za ta ci gaba da bibiyar neman Alvarez bayan gasar Kofin Duniya, kuma tana iya haɗawa da ɗaya daga cikin 'yan wasanta a cikin yarjejeniyar.

Barcelona na son bai wa ɗan wasan gaba na Sifaniya, Ferran Torres mai shekara 26, sabon kwantiragi duk da sha'awar da Paris St-Germain (PSG) ke nuna masa. Sai dai ƙungiyar na shirin jira har zuwa watan Satumba saboda ƙa'idojin harkokin kuɗi.

Liverpool ta sake tuntuɓar Paris St-Germain kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na Faransa, Bradley Barcola mai shekara 23, a bazaran nan.

Arsenal na ƙoƙarin sayar da ɗan wasan gabanta na Brazil, Gabriel Jesus, inda AC Milan ke cikin manyan ƙungiyoyin da ke sha'awar sayen ɗan wasan mai shekara 29.

Sunderland na gab da kammala sayen ɗan wasan baya na dama na Belgium, Thomas Meunier mai shekara 34, bayan ya bar ƙungiyar Lille.

Liverpool ta yi watsi da sabon tayin da aka gabatar mata kan Curtis Jones. Tayin da Inter Milan ta inganta, wanda ya kai kusan fam miliyan 27, bai kai farashin fam miliyan 30 da Liverpool ke nema kan ɗan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 25 ba.

Everton ta ƙara ƙaimi wajen zawarcin ɗan wasan baya na Ingila mai taka leda a tawagar Ingila ta matasan ƙasa da shekara 21, Brooke Norton-Cuffy mai shekara 22 na ƙungiyar Genoa, bayan sabuwar tattaunawa kan yiwuwar ɗaukarsa.

Kyaftin din Tottenham, Cristian Romero mai shekara 28, na dab da barin ƙungiyar a wannan bazarar, yayin da Barcelona ke nuna sha'awar ɗan bayan na Argentina.

Wakilan ɗan wasan gaba na Netherlands, Crysencio Summerville mai shekara 24, sun gana da jami'an Roma kan yiwuwar komawarsa daga West Ham zuwa ƙungiyar ta Italiya.

Ana gwajin mai tsaron ragar Amurka, Gabriel Slonina mai shekara 22, a ƙungiyar Strasbourg domin duba yiwuwar komawarsa daga Chelsea.