Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 15/07/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Najeriya ta kammala kwashe ƴanƙasarta daga Afirka ta Kudu

    Hukumomin Najeriya sun kammala kwashe ƴanƙasar daga Afirka ta Kudu bayan ƙazancewar zanga-zangar ƙyamar baƙi a ƙasar.

    A yau ne jirgi na ƙarshe kuma na shida ɗauke da ƴanƙasar 306 ya sauka a filin jirgin saman Legas.

    Zuwa yanzu fiye da ƴan Najeriya 1,200 ne hukumomin ƙasar suka kwaso a ƙarkashin nwani shirin gwamnatin ƙasar na mayar da ƴanƙasar gida bayan ɓarkewar zanga-zangar ƙyamar baƙi..

    Zanga-zangar wadda a wasu yankunan ake yinta lafiya, ta ƙazance a wasu yankunan har da kisa.

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta nemi diyya daga gwamnatin Afirka ta Kudu ga ƴanƙasarta, waɗanda aka tilasta wa barin sana'o'insu da gidajensu da kuma kadarorinsu a Afirka ta Kudu

  2. Ƴanbinbiga sun sace ɗaliban da ke rubuta NECO a jihar Kogi

    Rundunar ƴansandan jihar Kogi ta tabbatar da yin garkuwa da ɗalibai huɗu da ke rubuta jarrabawar NECO da wasu malamai biyu cikin har da shugaban makarantar.

    Cikin wata sanarwar kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Salisu Oyiza ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da yamma lokacin da ɗaliban ke tsaka da rubuta jarrabawar NECO a makarantar Sakandiren Edo-Ekina da ke yankin ƙaramar hukumar Dekina.

    Ƴansan sun kuma ce sun kai ɗaukin gaggawa tare da ƙaddamar da bincike kan lamarin.

    “Tawagar hadin giwar jami'an tsaro sun gaggauta ƙaddamar d aneman ɗaliban, waɗanda har yanzu kuma suna neman jami'an'', in ji sanarwar.

    ASP Oyiza ta ce zuwa yanzu jami'an tsaro sun kuɓutar da ɗalibi ɗaya, yayin da suke ci gaba da neman sauran tare da farautar maharan.

    Lamarin na zuwa kwanaki bayan kuɓutar da ɗaliban makarantar jihar Oyo da suka kwashe makonni a hannun ƴanbindiga.

  3. Iran ta yi barazanar rufe hanyoyin fito na ƙasashen Gulf

    Dakarun juyin juya halin Iran sun yi barazanar rufe duka hanyoyin da ƙasashe ƙawayen Amurka ke fitar da kayyakinsu zuwa ƙetare a matsayin martani ga datse tasoshin ruwanta da Amurka ke yi.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar sa'o'i bayan da Amurka ta sanar da datse tasoshin ruwan, ta ce za ta lalata hanyoyin fiton kayayyaki da ƙasashe ƙawayen Amurka ke amfani da su, idan aka ci gaba da toshe wa Iran hanyoyin fitar da manta.

    "Tun da aka datse wa Iran hanyoyin fitar da mai da iskar gas ɗinta domin durƙusar da tattalin arzikinmu, wadda ke zama barazana ga tattalin arzikin ƙawayen Amurka, to muma a jira namu matakin na datse hanyoyin fiton ƙasashen'', in ji sanarwar da IRGC.

  4. An yanke wa sojan Isra'ila hukuncin ɗaurin shekara biyar

    Rundunar sojan Isra'ila ta ce ta yanke wa wani sojanta hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari saboda samunsa da laifin aika wa wasu jami'an Iran bidiyon yadda sojojin Isra'ila ke kakkaɓo makaman linzami.

    Sojojin Isra'ilar sun ce sojan ya aika bidiyoyi guda biyu waɗanda ''aka biya shi kuɗin tura su'' a lokacin yaƙin kwana 12 tsakanin ƙasashen biyu.

    Haka kuma rundunar sojin Isra'ila ta ce ta same shi da wasu bidiyoyin d ya naɗa a biranen Isra'ila, waɗanda ya aika su ga jami'an na Iran.

    A lokacin yaƙin, Isra'ila ta hana ɗaukar bidiyon wasu keɓantattun wuraren da yaƙi ya lalata.

  5. Amurka na goyon bayan farfaɗo da bututun man Iraƙi da Siriya

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce tana goyon bayan ƙoƙarin da Iraƙi da Siriya ke yi na farfaɗo da wani bututun ɗanyen mai da ya haɗa ƙasashen biyu.

    Wannan na daga cikin jerin matakai da aka sanar a baya-bayan nan don rage tasirin matakin da Iran ta ɗauka na hana jirage ruwa ratsawa ta mashigin Hormuz.

    Wani jami'i ya ce kamfanonin mai na Amurka za su taka rawa wajen sabunta aikin bututun man fetur na Kirkuk-Baniyas, wanda ya kusan daina aiki gaba ɗaya tun bayan mamayar da Amurka ta yi wa Iraƙi a shekarar 2003.

    Shugaba Trump ya ce Iraki za ta iya taka muhimiyar rawa saboda tana da arzikin man fetur kuma za su kulla yarjejeniyoyi da dama da ita.

    Ana sa ran wannan bututun zai riƙa jigilar ɗanyen man fetur daga filayen man Iraki zuwa gaɓar tekun Bahar Rum da ke Siriya.

  6. Mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe - Iran

    Dakarun juyin juya halin Iran sun ce mashigin Hormuz zai ci gaba da kasancewa a rufe, har sai Amurka ta dakatar hare-haren da take kaiwa ƙasar , kwana guda bayan da sojojin Amurka suka sake toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran.

    Dakarun sun yi gargaɗin cewa za su iya faɗaɗa hare-haren da suke kaiwa zuwa wasu hanyoyin fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje.

    Ɓangarorin biyu sun sake musayar hare-hare cikin dare, inda kafafen yaɗa labaran Iran suka ce an kai farmaki kan cibiyoyin Amurka da ke Bahrain da Kuwait da Jordan.

    Sojojin Amurka sun ce sun shafe tsawon sa'a bakwai suna kai wa Iran hari .

    Yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ke rushewa, Shugaba Trump ya sake yin barazanar kai hare-hare kan tashoshin lantarki da gadoji a Iran idan ba ta koma teburin tattaunawa ba.

  7. Assalama alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan shafi domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta da muhawara kan labaran da muke wallafawa.