Fernandes ya taka rawar gani a wasan Leicester a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta doke Leicester City 3-0 a wasan mako na 11 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.
United ta fara cin ƙwallo ta hannun Bruno Fernandes a minti na 17 da take leda, kenan ɗan kasar Portugal yana da hannu a zura ƙwallo 100 a wasa na 170 da ya yi wa United.
United ta kara na biyu ta hannun Kristiansen wanda ya ci gida, daga baya Garnacho ya zura na uku a raga saura minti takwas a tashi daga karawar.
Da wannan sakamakon United mai maki 15 tana ta 13 a teburin Premier, ita kuwa Leicester City tana ta 15 da maki 10, bayan karawar mako na 11.
Wannan shi ne wasan karshe da kociyan riƙon ƙwarya, Ruud van Nistelrooy ya ja ragama, kuma karo na biyu da ya doke Leicester City.
Ranar Laraba 30 ga watan Oktoba, United ta yi waje da ƙungiyar King Power daga Carabao Cup da cin 5-2 a Old Trafford.
Tun bayan da United ta kori Erik ten Hag ta naɗa Nistelrooy aikin riƙon kwarya, ya doke Leicester a League Cup da yin 1-1 da Chelsea a Premier League.
Haka kuma a karkashin sa ne United ta doke PAOK Salonika 2-0 ranar Alhamis 7 ga watan Nuwamba a Europa League a Old Trafford.
Ranar Lahadi 24 ga watan Nuwamba, United za ta je gidan Ipswich Town a wasan mako na 12 a Premier League tare da sabon kociya, Rubin Amorim.
Daga nan kuma United za ta karɓi bakuncin Bodo Glimt a Europa League ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba.










