Kluivert ya zama na farko a Premier da ya ci uku rigis a bugun fenariti

Justin Kluivert

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Justin Kluivert ya zama na farko a shekara 67 da ya ci ƙwallo uku rigis a bugun fenariti a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar.

Bournemouth ce ta je ta doke Wolverhampton 4-2 a wasan mako na 13 da suka fafata a Molinuex.

Haka kuma dan wasan Bournemouth, Evanilson ya zama na farko a gasar Premier League da ya samo bugun daga kai sai mai tsaron raga karo uku a wasa.

Kluivert ya ci bugun fenaritin ne a minti na uku da take leda da a minti na 18 da kuma a minti na 74, sai Bournemouth ta kara na hudu ta hannun Kerkez.

Larsen na Wolverhampton shi ne ya zura kwallo biyu a ragar Bournemouth.

Kawo yanzu Kluivert ya zura ƙwallo biyar a gasar Premier League a kakar nan, bayan da ya fara cin Arsenal ɗaya ranar 19 ga watan Oktoba da Brentford ranar 9 ga watan Nuwamba.

Bournemouth za ta karbi bakuncin Tottenham ranar Alhamis 5 ga watan Disamba a Premier League daga nan ta je Ipswich ranar Lahadi 8 ga watan Disamba.