Manchester United na neman Ndidi, Tottenham da Newcastle na hamayya kan Grealish

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 28, wanda rahotanni ke cewa ya na ɗauke da farashin fam miliyan 9 a kwantiraginsa da Leicester City, yayin da Fulham da Everton da kuma Crystal Palace su ka nuna sha'awarsu kan ɗan wasan . (Tuttosport)
Tottenham da Newcastle da Napoli duk suna bibiyar ɗan wasan tsakiya na Ingila Jack Grealish bayan da Manchester City ta sanya farashin fam miliyan 40 kan ɗan wasan mai shekara 29. (Sun)
Newcastle United na ci gaba da fatan cimma nasara a zawarcin da ta ke yi wa Marc Guehi, mai shekara 24, inda ƙungiyar ke neman ƙarfafa tawagar ƴan wasanta da ɗan wasan bayan na Ingila da Crystal Palace. (GiveMeSport)
Crystal Palace na tattaunawa da Sporting kan tayin fam miliyan 45 da za ta gabatar kan ɗan wasan bayan Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 21. (Guardian)
Har ila yau Crystal Palace na zawarcin ɗan wasan bayan Italiya Davide Calabria, mai shekara 28. Ya taka rawar gani a zaman aro da ya yi a Bologna a kakar wasan da ta wuce amma ya kasance ɗan wasa mai zaman kansa bayan ya bar AC Milan lokacin da kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen kakar wasan. (Sky Sports)
Manchester United ta fara zawarcin ɗan wasan Atalanta da Brazil Ederson, yayin da ƙungiyoyin Serie A Inter Milan da Juventus suma su ke bibiyar ɗan wasan mai shekara 26 wanda ke ɗauke da farashin fam miliyan 44. (Goal)
Ɗan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, ba ya tunanin barin Manchester United sai dai idan ƙungiyar ta yanke shawarar sallamarsa, inda Inter Milan ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka nuna sha'awarsu kan ɗan wasan. (Fabrizio Romano)
A halin da ake ciki kuma, Manchester United ta sanya farashin fam miliyan 30 kan Andre Onana yayin da ta ke tattaunawa da AS Monaco a ƙarshen watan da ya gabata, amma alamu na nuna cewa golan Kamaru mai shekara 29 na iya ci gaba da zama a ƙungiyar ta Old Trafford (Mail)
Newcastle ta fara tattaunawa da Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 28, bayan koci Eddie Howe ya bayyana cewa ya daɗe yana sha'awar ɗan wasan na Ingila wanda ya bar Everton bayan kwantiraginsa ya ƙare a watan da ya gabata. (Talksport)
Sunderland da Leeds United da kuma Wolves suna zawarcin ɗan wasan Lens da Morocco Neil El Aynaoui na kasa da shekaru 23, amma suna fuskantar hamayya daga AS Roma da Juventus da AC Milan kan ɗan wasan mai shekara 24 (Footmercato).
Kocin Slavia Prague Jindrich Tripisovsky ya tabbatar da cewa El Hadji Malick Diouf na shirin barin ƙungiyar a daidai lokacin da West Ham da Leeds ke zawarcin ɗan wasan bayan na Senegal mai shekara 20. (Standard)
Ɗan wasan bayan West Ham da Morocco Nayef Aguerd, mai shekara 29, ya kasance kan gaba a jerin ƴan wasan da ƙungiyar Marseille ta Faransa ke zawarci a bana. (L'Equipe)












