Ancelotti ya ci wa Real Madrid wasa na 200 a gidan Osasuna

Asalin hoton, Real Madrid FC
Carlo Ancelotti ya yi nasara ta 200 ranar Asabar a wasan mako na 29 da Real Madrid ta caskara Osasuna 4-0.
Dan kasar Italiya ya yi wannan bajintar a karawa 277 a kaka biyar da yake jan ragamar Real Madrid.
Haka kuma karawar da aka yi a filin wasa na El Sadar shi ne na 900 da Ancelotti ke horar da tamaula a matakin koci.
Cikin wasa 200 da Ancelotti ya ci a Real Madrid ya hada da 129 a La Liga da 43 a Champions League da 18 a Copa del Rey da hudu a Sifanish Super Cup.
Sauran nasarorin da ya yi har da hudu a Club World Cup da kuma biyu a European Super Cup.
Kawo yanzu Ancelotti shi ne na biyu a matakin koci da ya ci wasa da yawa a Real Madrid, bayan Miguel Muñoz, mai cin wasa 357.
Tuni dai dan kasar Italiya ya lashe Champions Leagues biyu da Club World Cups biyu da European Super Cups biyu da La Liga daya da Copas del Rey biyu da kuma Spanish Super Cup.







