Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mataimakin Ten Hag zai bar Manchester United
Ɗaya daga cikin masu taimaka wa Eric Ten hag a Man United, Eric Ramsay zai bar ƙungiyar ta ingila domin ya karɓi aikin kocin ƙungiyar Minnosita United da ke wasa a gasar MLS ta Amurka.
Ramsay ya kasance a tawagar masu horas da United tun bayan komawarsa daga Chelsea kuma zai bar ƙungiyar bayan wasan hamayya na Manchester derby a filin wasan Etihad.
"Na yi matukar farin cikin komawa ƙungiyar da ke da irin wannan al'adar ƙwallon ƙafa mai ƙarfi, da ke da magoya baya masu matuƙar kishi.'' In ji shi.
Ya ƙara da cewa "Na yi magana da ma'aikatan kulob din a yayin da ake gudanar da wannan tattaunawar kuma na ji sha'awar kowa da kowa ke da zummar ciyar da kulob ɗin gaba.''
United ta ce ba za a maye gurbin Ramsay cikin ƙanƙanin lokaci ba, inda mahukunta suka ce za a raba ayyukansa a tsakanin sauran tawagar ƙarƙashin koc Erik ten Hag.