Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kimpembe ya nemi afuwar magoya bayan PSG
Mai tsaron bayan Paris St-Germain, Presnel Kimpembe ya nemi afuwar magoya baya, sakamakon doke su 3-1 da Monaco ta yi.
Ya yi hakan ne bayan tashi daga karawat ta Ligue 1, wanda ya karbi bututun magana ya kuma nemi afuwa kan doke su da aka yi a gidan Monaco.
Monaco ta ci kwallayen ta hannun Aleksandr Golovin da kuma Wissam Ben Yedder, wanda ya zura biyu a raga.
Ita kuwa PSG ta zare daya ta hannun Warren Zaire-Emery a babbar gasar tamaula ta Faransa ta mako na 23.
PSG, wadda ta buga wasan ranar Asabar ba tare da Kylian Mbappe da Lionel Messi da kuma Marco Verratti ba, ta yi rashin nasara ta biyu cikin kwana hudu kenan.
PSG za ta karbi bakuncin Bayern Munich ranar Talata a Champions League karawar kungiyoyi 16 da suka rage, kuma a karawar farko.
Mbappe ba zai buga wasan na ranar Talata da Bayern ba, sakamakon jinya da yake yi.
Kociyan PSG, Christophe Galtier na fatan Messi ya murmure da wari domin fuskanttar kungiyar Jamus, wanda ya ji raunin da ya hana shi buga fafatawa da Monaco.
A watan jiya ne PSG ta maye gurbin mukamin mataimakin kyaftin daga wajen Kimpembe ya koma ga Mbappe.
PSG ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Ligue 1 da tazarar maki biyar tsakaninta da Marseille ta biyu, ita kuwa Monaco tana ta uku mai maki 47.
PSG ta yi rashin nasara a karawa uku a lik a 2023, wadda Marseille ta yi waje da ita a French Cup ranar Laraba.