Real ta fitar da Liverpool a Champions League na bana

An wallafa

Real Madrid ta doke Liverpool da cin 1-0 a wasa na biyu a Champions League, zagayen 'yan 16 da suka kara a Santiago Bernabeu.

Karim Benzema ne ya ci wa Real kwallon da take bukata, ta kuma kai zagayen daf da na kusa da na karshe.

Kenan kungiyar Sifaniya ta fitar da ta Ingila da cin 6-2 a karawa gida da waje a bana.

Ranar 21 ga watan Fabrairu, Real ta ci Liverpool 5-2 a wasan farko a Anfield a gasar zakarun Turai ta bana.

A bara Real ta doke Liverpool 1-0 a Faransa ta dauki Champions League na 14 jimilla, karo na biyu da ta dauki kofin a kan Liverpool a tarihi.

A kakar 2017/18, Real ta ci Liverpool 3-1 a Lisbon ta lashe Champions League.

Sun yi wasa 11 a tsakaninsu, Real ta ci bakwai, Liverpool ta yi nasara a uku da canjaras daya.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki tara tsakaninta da Barcelona ta biyu a bana, ita take rike da Champions League.

Ranar 19 ga watan Maris, Real za ta ziyarci Barcelona a gasar La Liga da za su buga a Camp Nou, karawar hamayya ta El Clasico.

Ita kuwa Liverpool tana ta shida a Premier League da maki 42, bayan da Arsenal ke jan ragama mai maki 66, bayan wasan mako na 27.

Sai a ranar 1 ga watan Afirilu Liverpool za ta ziyarci Manchester City, domin buga wasan Premier League a Etihad.

Tun farko an dage karawar da Liverpool ya kamata ta buga da Fulham ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Jerin wasa da aka buga tsakanin kungiyoyin biyu:

2022/2023 Champions League

  • Real Madrid. 1 - 0. Liverpool
  • Liverpool 2 - 5 Real Madrid

2021/2022 Champions League

  • Liverpool 0 - 1 Real Madrid

2020/2021 Champions League

  • Liverpool 0 - 0 Real Madrid
  • Real Madrid 3 - 1 Liverpool

2017/2018 Champions League

  • Real Madrid 3 - 1 Liverpool

2014/2015 Champions League

  • Real Madrid 1 - 0 Liverpool
  • Liverpool 0 - 3 Real Madrid

2008/2009 Champions League

  • Liverpool 4 - 0 Real Madrid
  • Real Madrid 0 - 1 Liverpool

1980/1981 European Cup

  • Liverpool 1 - 0 Real Madrid

Liverpool na fuskantar kalubale a kakar bana, wadda take ta shida a teburin Premier League.

Watakila Liverpool za ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi koda na shayi ba, za ta mayar da hankali kan kare kakar bana cikin 'yan hudu a Premier, hakan zai ba ta damar buga Champions League a badi.

A bara Liverpool ta dauki Carabao da FA Cup, sannan ta yi ta biyu a Premier League ta kuma je wasan karshe a Champions League.