Haaland ya ci gaba da kafa tarihi a yawan cin kwallaye

An wallafa

Erling Haaland ya zama kan gaba a cin kwallaye a Manchester City a kaka daya kamar yadda yake ci gaba da kafa tarihi a fagen taga leada.

Dan wasan tawagar Norway ya ci biyar rigis a karawar da City ta doke RB Leipzig 7-0 a Champions League.

Kungiyar Etihad ta kai zagayen gaba da cin kwallo 8-1, bayan da suka tashi 1-1 cikin Fabrairu a wasan farko zagayen 'yan 16 a gasar zakarun Turai.

Tun bayan da ya koma City kan fara kakar bana, Haaland ya zura kwallo 39 a raga a wasa 36 a dukkan fafatawa da ya yi mata.

Ya doke tarihin yawan cin kwallaye da Tommy Johnson ya kafa a City na shekara 94 a kungiyar.

Haaland ya ci kwallo 22 a wasa 12 a Champions League a gida.

Kwallo biyar da ya zura a ragar Leipzig ranar Talata ya zama na uku da ya yi wannan bajintar a gasar, bayan Lionel Messi a Barcelona a wasa da Bayer Leverkusen a 2012 da Luiz Adriano a Shakhtar Donetsk a karawa da BATE Borisov a 2014.

Kawo yanzu Haaland ya zura kwallo 33 a wasa 25 a Champions League, ya zama matashin da ya ci kwallo sama da 30 mai shekara 22 da kwana 236.

Mai tarihin a baya shine Kyalian Mbappe, wanda ya haura Haaland da kwana 116.

Haaland yana da kwallo 10 a Champions League a bana, shine kan gaba a cin kwallaye a kaka daya a City a gasar zakarun Turai.

Tsohon dan wasan Red Bull Salzburg da Borussia Dortmund ya ci kwallo da yawa a gasar zakarun fiye da Wayne Rooney da Kaka da kuma Samuel Eto'o.