Ko Osimhen zai koma buga Premier League kuwa?

An wallafa

Victor Osimhen ya zama dan wasan da kowacce kungiya a Turai za ta yi fatan ta mallaka, bayan rawar da yake takawa a bana a Napoli.

Dan kwallon tawagar Najeriya ya ce yana mafarkin wata rana ya buga Premier League - ko hakan zai tabbata nan gaba?

Napoli na taka rawar gani a bana, wadda take jan ragamar teburin Serie A da tazarar maki 18, tana kuma daf da zuwa quarter finals a Champions League.

Napoli za ta karbi bakuncin Eintracht Frankfurt ranar Laraba a wasa na biyu zagayen 'yan 16 a gasar zakarun Turai.

A wasan farko da suka buga a gasar cikin Fabrairu a Jamus, Napoli ce ta yi nasara da cin 2-0.

Osimhen shine kan gaba a yawan cin kwallaye a Serie A mai 19 a raga a wasa 22 da tazarar biyar tsakaninsa da Lautaro Martinez na Inter Milan.

Dan wasan Manchester City, Erling Haaland da na Tottenham, Harry Kane ne ke gabansa a cin kwallaye a manyan gasar Turai biyar a kakar nan.

Lamba tara ne da ya kware a cin kwallo idonsa idon raga, mai tsawon sama da kafa shida.

Osimhen, wanda ya taka leda a Wolfsburg da Charleroi da kuma Lille, ya koma Napoli a 2020, wanda kwanan nan ya ce yana mafarkin buga Premier League.

''Mutane da dama a duniya na cewar Premier League ce gasa mafi martaba a duniya, amma yanzu ina murza leda a fitatciyar gasa a duniya, wato Serie A.''

To sai dai wasu na ganin komawa buga Premier League ba abu ne mai sauki ba, karkashin shugaban Napoli, Aurelio de Laurentiis, wanda yake da wuyar sha'ani wajen sayar da fitatcen dan kwallon da yake da shi.

Wani dan jarida a Italiya, wanda ya kware a bibiyar tamaula ya sanar da BBC cewar Osimhen ya kai darajar kudi sama da fam miliyan 89 zuwa fam miliyan 133.

Neymar ne da Kylian Mbappe aka saya sama da fam miliyan 133 kowanne a Paris St Germain, kenan da wuya idan za a dauke shi a irin wannan farashin.

Dan wasan da aka saya mafi tsada a Premier League a tarihi shine, Enzo Fernandez da Chelsea ta dauko daga Benfica a Janairu kan fam miliyan 107.

Shin wacce kungiya ce za ta fi dacewa da salon taka ledar Osimhen a Premier League?