Chelsea za ta nemi Benzema ko Firmino Ratcliffe zai yi sauyi a Man Utd idan ciniki ya faɗa

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Sir Jim Ratcliffe na son sayen tauraron ɗan gaba wanda ya kai Harry Kane na Bayern Munich , da zarar hukumar gasar Premier ta amince masa ya sayi kashi 25 cikin ɗari na hannun jarin Manchester United. (Standard)

Wataƙila Chelsean ta nemi Karim Benzema daga Al-Ittihad ta Saudiyya ko kuma Roberto Firmino na Brazil, wanda shi ma ya tafi Al-Ahli ta Saudiyyar a bazara. (Goal)

Newcastle ta haƙura da neman ɗan wasan tsakiya Kalvin Phillips, ɗan Ingila saboda buƙatar Manchester City ta neman a biya ta kuɗin aronsa. (Telegraph )

Bayan Newcastle, Crystal Palace, da Everton, da West Ham da kuma Juventus dukkanninsu suna son Phillips. (Sky Sports)

Paris St-Germain na nazari kan sayen ɗan wasan tsakiya na Newcastle, Bruno Guimaraes ɗan Brazil wanda yarjejeniyarsa ta tanadi duk ƙungiyar da ke sonshi sai ta lale fam miliyan 100. (Talksport)

Manchester United ta tattauna kan yuwuwar sayen matashin ɗan wasan gaba na gefe Michael Olise, na Ingila mai shekara 22, a bazara, kuma a shirye take ta bar ɗan bayanta na Ingila Aaron Wan-Bissaka, ya tafi ƙungiyar ta Olise, Crystal Palace. (ESPN)

Haka kuma Red Devils ɗin sun bi Bayern Munich zawarcin matashin ɗan bayan Barcelona, Ronald Araujo na Uruguay mai shekara 23. (Florian Plettenberg)

Wataƙila ɗan wasan tsakiya Renato Sanches ɗan Portugal ya bar Paris St-Germain a watan nan, saboda ƙungiyar ba ta son dawo da shi daga aron da ta bayar da shi ga Roma wadda ita ma tana son rabuwa da shi. (Fabrizio Romano)

Bisa ga dukkan alamu Jesse Lingard, wanda ba shi da ƙungiya zai tafi gasar Amurka (MLS), kuma tuni sabon wakilinsa na tattaunawa da ƙungiyar Portland Timbers a ƙoƙarin da ɗan wasan na tsakiya na Ingila ke yi na komawa kan ganiyarsa. (Mail)

Wataƙila Chelsea ta nemi aron ɗan gaban Aston Villa Jhon Duran na Colombia mai shekara 20, na ɗan gajeren lokaci. (Nathan Gissing daga Metro)

Ana sa ran Chelsea ta buƙaci a biya ta fam miliyan 35 wato gaba ɗayan kuɗin da duk wata ƙungiya da ke son sayen ɗan bayan Holland Ian Maatsen, mai shekara 21, wanda yanzu yake zaman aro a Borussia Dortmund, za ta biya. (Telegraph )

Celtic na son golan Liverpool Caoimhin Kelleher, amma kuma za ta iya fuskantar gogayya daga Brentford, da Brighton da Wolves a kan mai tsaron ragar na Jamhuriyar Ireland. (Mail)