Messi ya zama gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na 2023

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya lashe ƙyautar gwarzon kwallon kafa na duniya na Fifa na 2023 a wani biki da aka gudanar a Landan ranar Litinin.
Kyaftin din tawagar Argentina ya yi takara tare da Kylian Mbappe na Paris St Germain da Erling Haaland na Manchester City.
Mai tsaron ragar Man City, Ederson shi ne ya lashe kyautar golan da ba kamarsa a bara, bayan takara da Thibaut Courtois na Real Madrid da na Al Hilal, Yassine Bounou.
City ta lashe kofi uku a kakar da ta wuce, wadda ta dauki Premier League da Champions League da kuma FA Cup a 2022-23.
Messi, mai shekara 36 ya fara kakar 2023 a Paris St-Germain daga nan ya koma buga gasar kwallon Amurka a Inter Miami a watan Yuni.
Ya kuma lashe ƙyautar a karo na uku a tarihi tun bayan da aka fara bikin a 2016, wanda ya lashe a 2019 da kuma 2022.
Ya ci kwallo tara a PSG da kungiyar ta dauki Ligue 1 da kuma zura kwallo 10 a raga a wasa bakwai a Inter Miami da ta lashe kofin farko a tarihi, League Cup.
Haaland ya ci kwallo 36 a Premier League a bara - ya zura 52 a dukkan fafatawa a 2022/23 - 28 daga ciki bayan gasar kofin duniya da guda biyu a bana kafin 20 ga watan Agusta.
Shi kuwa Mbappe ya lashe Ligue 1 a PSG, kuma shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a babbar gasar kasar Faransa.
Mai shekara 25 ya ci kwallo 18 a PSG tsakanin 19 ga watan Disambar 2022 zuwa 20 ga watan Agustan 2023.
A fanni mata kuwa Aitana Bonmati ce ta lashe ƙyautar gwarzuwar ƙwallon kafa ta duniya ta Fifa ta bara.
Ƴar wasan ta taka rawar gani da Barcelona ta lashe Champions League da kuma tawagar Sifaniya da ta dauki kofin duniya a Australia da New Zealand.
Ta kuma yi takara ne da Linda Caicedo ta Colombia da Real Madrid da kuma Jenni Hermoso ta Sifaniya da Pachuca.
An auna kwazon gwarzon bana da wanda zai karbi kyautar Puskas - a fannin taka leda daga 19 ga watan Disambar 2022 zuwa 20 ga watan Agustan 2023.
Za kuma a auna ƙwazon mata daga 1 ga watan Agustan 2022 zuwa 20 ga watan Agustan 2023.










