Lima ya kawo ƙarshen shekara 26 yana buga wa Andorra tamaula

Ildefons Lima

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Bayan shekara 26 da yi wa Andorra wasa 137, Ildefons Lima ya yi ritaya daga buga wa tawagar tamaula.

Mai shekara 43 ya fara yi wa Andora wasa yana da shekara 14 a karawar da Estonia ta doke su 4-1 a 1997.

Tun daga lokacin ya buga wa Andorra dukkan karawa, kuma ranar Talata ya yi wasan ƙarshe da Switzerland ta yi nasara da ci 3-0.

An canja ɗan wasan a minti 23, an kuma yi ta masa tafi tsakanin magoya bayan Switzerland da Andorra lokacin da zai fita daga filin.

Ricard Fernandez Betriu ne ya canje shi, wanda aka haifa shekara biyu ttsakani, bayan da Lima ya fara buga wa Andorra tamaula.

A shekarar 2021 Guinness World Recors ta bayyana Lima a matakin wanda ke kan gaba a yawan buga wa tawagar kasa tamaula a tarihi.

Macen da ta dade tana buga wa kasarta tamaula a duniya ita ce Formiga ta Brazil, mai shekara 45, wadda ta yi shekara 26 da buga karawa 234 tsakanin 1995-2021.