Lyon ta kori kociyanta Laurent Blanc

Asalin hoton, Getty Images
Lyon ta kori kociyanta, Laurent Blanc bayan da take kasan teburin Ligue 1.
Wasan da ya ja ragama na karshe shine wanda Paris St Germain ta ci 4-1 a babbar gasar tamaula ta Faransa ta bana.
Lyon ta samu maki daya daga wasa hudu da ta buga da fara wasannin bana, daya daga kaka mafi muni da kungiyar ta fuskanta.
An bai wa daraktan tsare-tsaren kungiyar Jean Francois Vulliez aikin rikon kwarya, wanda ya horar da makarantar kungiyar.
Blanc, mai shekara 57 ya zama kociyan Lyon cikin watan Oktoba, wanda ya ja ragamar kungiyar ta kare a mataki na bakwai a teburin kakar bara.
Aikin koci na farko da ya yi kenan, tun bayar da ya bar Paris St Germain a 2015-16, koda yake ya horar da Al Rayyan ta Qatar a matakin rikon kwarya.
Blanc ya lashe kofin Ligue 1 a PSG da lokacin da ya ja ragamar Bordeaux.
An bayar da rahoton cewar tsohon kociyan Brighton da Chelsea, Graham Potter, mai shekara 48, bai amince da tayin horar da Lyon da aka yi masa a makon jiya ba.
Gennaro Gattuso, mai shekara 45, yana cikin wadanda ake alakantawa da aikin jan ragamar Lyon, bayan da ya bar Valencia a watan Janairu.














