Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aston Villa za ta ɗauki Onana na Everton kan £50m
Aston Villa ta yi nisa wajen cinikin Amadou Onana daga Everton kan kudin da zai kai £50m.
Mai shekara 22 ya buga wa Belgium Euro 2024 a Jamus, ya kuma samu damar da zai kara a gasar Champions League da za a buga a bana.
Onana ya koma taka leda a Everton daga Lille kan £33m a Agusta 2022, wanda ya yi karawa 72 da cin ƙwallo hudu.
Villa za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da ta kammala a mataki na huɗu a kakar da ta wuce ta Premier League.
Wakilan Arsenal sun tattauna da na Onana tun farkon shekarar nan, amma ba su kai ga cimma ƙwantiragi ba.
An fahimci cewar tayin da Villa ta yi ya yi daidai da ƙudin da Everton za ta iya sayar da ɗan wasan, wanda Manchester United ke sha'awar ɗaukar.
Wanda aka haifa a Senegal ya taka leda a Hamburg, bayan Hoffenheim, wanda ya fara daga ƙaramar makarantar Anderlecht a Belgium.
Villa ta shiga kasuwa domin sayen mai taka leda daga tsakiya, tun bayan da ta sayar da Douglas Luiz ga Juventus kan £42.35m a watan jiya.