Gwamnatin jihar Niger ta saka dokar hana fita a Lambata

.

Asalin hoton, Niger state Government

An wallafa

Gwamnan jihar Niger da ke arewa ta tsakiyar Najeriya Abukakar Sani Bello ya sanya dokar hana fita a garin Lambata, da ke yankin ƙaramar hukumar Gurara a jihar, bayan da wani rikici ya ɓarke a garin, wanda ya yi sanadin mutuwar Dagacin garin Mohammed Abdulsafur.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim matane ya fitar, ya ce sakamakon abin da ya faru, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin saka dokar hana fita a garin Lambata daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

A cewar sanarwar dokar za ta fara aiki ne daga yau Lahadi 15 ga watan Janairu har zuwa wani lokaci da za ta sanar a nan gaba.

Ahmed Matane ya ce an sanya dokar hana fitar ne domin taimaka wa jami'an tsaro daidai al'amura tare da kwantar da tarzoma a yankin, da kare rayuka da kuma jami'an damar maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Sakataren gwamnatin ya kuma gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan rikicin da ya auku a garin na lambata.

Haka kuma gwmanatin jihar ta yi kira ga mazauna yankin da su bai wa jami'an tsaro haɗin kai domin maido da zamn lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare da yin kira ga jami'an tsaro da su tabbatar sun an bi dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya.

Jihar Niger dai na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci, da ayyukan 'yan bindiga.