Kirsimeti: Fafaroma ya nuna damuwa kan 'tasirin yunwa da neman kudi da iko'

Asalin hoton, Reuters
Shugaban cocin Katolika Fafaroma Francis ya yi tir da halayyar dan Adam da ta janyo "yunwa da neman kudi da iko", a cikin sakonsa na jajibirin bikin Kirsimeti da ya saba fitarwa a fadar Vatican.
Da alama Fafaroman na magana ne kan yakin da ake ci gaba da gwambzawa a Ukraine da kuma sauran manyan rikice-rikice a fadin duniya:
"Yake-yake nawa muka gani?"
Ya ce gajiyayyu ne wadannan rikice-rikicen suka fi yi wa illa, "Halin da yaran da yaki da talauci da kuma rashin adalci suka mamaye ne nafi tunani a kai."
Ya yi wannan jawabi ne cikin sakon da ya mika kai tsaye ga masu ibada da suka hallara a cocin St Peter Basilica na Vatican City.
Fafaroma Francis mai shekara 86 ya isa cocin ne bisa wata keken masu lalurar kafa.
Sai dai bai fito fili ya ambaci yakin na Ukraine ba.
Ranar 25 ga kowace shekara Kiristoci a dukkan sassa na duniya ke yi bukukuwan Kirsimeti domin tunawa da haihuwar Isa Almasihu.









