Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗan bindiga ya tsere bayan ya harbe mutum 10 a Amurka
An kashe mutum 10 sakamakon harbe-harben da aka yi a wani zauren rawa na Monterey Park da ke birnin California a Amurka.
'Yan sanda sun ce an jikkata wasu mutum 10 kuma wanda ake zargi da kisan ya tsere.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:20 na daren Asabar agogon yankin (ƙarfe 5:20 ranar Lahadi agogon Najeriya da Nijar).
Wani da abin ya faru a kan idonsa ya faɗa wa jaridar Los Angeles Times cewa mutane sun afka shagonsa na cin abinci suna ce masa ya gaggauta rufewa saboda akwai wani mutum ɗauke da mashinga a kusa da wurin.
"Da alama lamarin ya faru a kusa da wani zauren rawa, inda wani ɗan bindiga ya zo da wata mashinga, bindigar da ke harba harsasai da yawa kan mutanen da akasarinsu 'yan nahiyar Asiya ne," kamar yadda mai aika rahoto Jeong Park ya faɗa wa BBC.
Wani shaidar gani da ido ya faɗa masa cewa wani mutum ya tsere daga wurin 'yan mintuna bayan harbe-harben a mota.
Dubban mutane sun taru don gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar 'yan China ta Lunar a birnin na Monterey Park.
Reshen 'yan sanda na Los Angeles ya ce suna neman wani namiji da ake zargi da harbe-harben wanda ya gudu daga wurin da lamarin ya faru, amma ba su ba da wani ƙarin bayani ba.
Masu bincike sun ce zuwa yanzu ba a iya gano dalilin da ya jawo harbe-harben ba kuma ya yi wuri a iya gane ko harin ƙiyayya ne.
'Yan sanda sun ce an dakatar da bukukuwan na Shekarar Lunar a ranar Lahadi. Kyaftin Andrew Meyer ya ce an ba su rahoton wani lamari a Alhambra da ke arewacin Montery Park, amma ba su ba da ƙarin bayani ba.
"Mun tura jami'an bincikenmu don tantance ko lamurran biyu na da alaƙa," a cewarsa.
Ba a raunata kowa ba a ɗaya lamarin na Alhambra amma 'yan sanda na wurin, kamar yadda kafar CBS ta ruwaito.
Wasu da ke halartar bikin sabuwar shekarar sun ce sun ji ƙarar abubuwan fashewa da suka zaci wasan tartsatsin wuta ne.
"Daga baya kuma sai na tabbatar ba wasa ba ne lokacin da na ji ƙarar jirgin helikwafta a sama. Saboda ba mu taɓa ganin helikwafta a nan ba," a cewar wani mai suna Gabriel yayin hirarsa da Reuters.