Mutumin da ya hallaka iyalansa saboda matarsa ta nemi ya sake ta

An wallafa

Ƴan sanda a birnin Utah na Amurka sun ce wani mutum mai shekara 42 ya kashe iyalansa su bakwai kafin daga baya ya kashe kansa.

Hakan ya biyo bayan ƙarar da matarsa ta shigar tana neman a raba aurensu.

A daren ranar Laraba ne aka gano gawar iyalan su takwas a gidansu da ke birnin Enoch, lokacin da ake gudanar da bincike.

Ƴan sanda sun ce a cikin waɗanda aka kashe akwai matar mutumin da mahaifiyarta da kuma ƴaƴansa biyar.

Jami'i mai tafiyar da lamurran birnin, Rob Dotson ya ce birnin mai yawan mutane 8,000 ya yi matukar kaduwa da labarin.

A lokaci wani taron manema labaru a ranar Alhamis, jami’an birnin sun ce mutumin mai shekara 42 mai suna Michael Haight ya buɗe wa matar tasa, mai suna Tausha, mai shekara 40 wuta da surukarsa Gail Earl mai shekara 78 sannan ‘ya’yansa biyar, kafin ya kashe kansa.

Yaran biyar da ba a bayyana sunansu ba, sun hada da mata uku da ke da shekara 17 da 12 da kuma 7 da yara biyu, daya dan shekara 7 da kuma dan sheara 4.

Babban jami'in birnin na Enoch, Rob Dotson ya ce ‘yan sanda ne suka gano gawarwakin nasu da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Laraba, bayan wani mutum ya yi koken cewa matarsa ta gaza samun aikin da aka tsara za a mata.

Wannan korafi ya sanya ‘yan sandan da ke tabbatar da jin dadin iyali da kuma kare dukiyoyinsu suka tafi gidan domin tabbatar da komai lafiya.

Mista Dotson ya ce duka wadanda aka kashen an samu raunin bindiga a jikinsu.

Jami’ai sun tabbatar da cewa matarsa ta shigar da karar neman saki tsakaninta da mijin nata a ranar 21 ga watan Disamba.

“Tausha mace ce mara matsala, ba ta taba fadin wani mummunan abu a kan kowa ba,” inji wata kawarta Tina Brown. “Ba ta da riko kuma tana yi wa mutane aiki da iyakar karfinta.”

Jami’an birnin ciki har da magajin garin, Jeffrey Chestnut, sun fito a hoton bidiyo jikkunansu sun yi sanyi lokacin da suke bayar da bayani kan halin da ake ciki.

“Kananan yaran sukan yi wasa a bayan gidana da ‘ya’yana,” in ji Chestnut.

Enoch wani karamin birni ne da ake noma ciki a yakin kudu maso yammaci, kuma yana da nissan kilomita 394 zuwa kudancin Birnin Salt Lake na ƙasar Amurka.

Yaran marigayin na zuwa wasu makarantu hudu ne a yankin Iron, kuma makarantun sun fitar da wata sanarwa da suka nuna damuwa game da mutuwar daliban nasu.

Tun daga nan ne kuma makarantun suka fara kawo kwararru a wajen sauya tunani domin sauran yara da suke karatu.

Gwamnan Utah, Spencer Cox ya aika sakon ta’aziyya ga wadanda wannan lamari ya shafa.

Matar shugaban kasar Amurka Jill Biden ita ma ta aika da tata ta’aziyyar, inda ta bayyana hakan a matsayin wani lamari mai cike da tashin hankali.