Barca ta kara bai wa Real tazarar maki a La Liga

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Barcelona ta ci Valencia 1-0 a wasan La Liga ranar Lahadi da suka kara a Camp Nou.

Raphinha ne ya ci wa kungiyar da Xavi ke jan ragama da kai, bayan da Sergio Busquets ya buga masa tamaula..

Ansu Fati ya buga kwallo amma ta bugi turki, kuma Barcelona ta karasa fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ronald Araujo jan kati.

an kore shi daga filin kai tsaye, bayan da ya yi wa Hugo Duro keta a karawar.

Golan Barcelona, Marc-Andre ter Stegen ya yi wasa 18 a karawa 24 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba a kakar nan.

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki 10 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.

Real za ta iya rage tazarar makin zuwa bakwai idan ta samu nasara a gidan Real Betis a yau Lahadi.

Barcelona ta buga fafatawwar ba tae da Robert Lewandowski da Ousmane Dembele ba, wadanda ke jinya da Pedri da aka dakatar da shi.

Shi kansa koci Xavi bai ja ragamar kungiyat ba, wanda shima aka dakatar da shi.

Valencia, wadda ta yi rashin nasara a Anfield tana nan a matakinta na 'yan kasan teburi a kakar nan..