Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe ya zama kan gaba a yawan cin kwallaye a PSG
Paris St Germain ta doke Nantes 4-2 a wasan mako na 26 a gasar Ligue 1 ranar Asabar.
Lionel Messi ne ya fara cin kwallo minti na 12 da fara wasa, sannan minti biyar tsakani PSG ta kara na biyu, bayan da Jaouen Hadjam ya ci gida.
Kafin hutu Nantes ta zare biyun ta hannun Ludovic Blas a minti na 31 da kuma ta biyun minti bakwai tsakani ta hannun Ignatius Ganago.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne PSG ta kara na uku ta hannun Danilo Pereira a minti na 60, sai Kylian Mbappe ya ci na hudu daf da za a tashi wasan.
Kwallo na 201 kenan da ya ci wa PSG tun bayan da ya koma kungiyar daga Monaco a 2017.
Hakan ya sa ya haura Edison Cavani, wadda shi ke rike da tarihin ci wa PSG kwallaye a tarihi.
Mbappe ya ci kwallo 30 a bana, ya kuma bayar da takwas aka zura a raga a wasa 247 da lashe kofin Ligue 1 hudu.
Dan wasan tawagar Faransa ya buga wa kasarsa gasar kofin duniya biyu da lashe daya a 2018 a Rasha, wanda ya karbi kyautar takalmin zinare a gasar 2022 a Qatar.
Argentina ce ta lashe kofin a bugun fanariti a Qatar karkashin kyaftin Messi, bayan da suka tashi 3-3.
Haka kuma Mbappe, wanda ya dauki Nations League tare da Faransa a 2021, bai taba daukar Champions League ba.