Ya Indiya za ta yi da wuraren bauta da kuma ayyukan raya kasa?

Tsaunukan bauta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai wuraren bauta da dama da mutane ke girmamawa a yankin Himalaya
An wallafa

Yankin Himalaya na kasar Indiya na da yawan wuraren ibada da ake girmamawa na ‘yan addinin Hindu kuma miliyoyin mutane na zuwa domin bauta a kowace shekara.

Yankin ya fuskanci bala’o’i daban-daban a ‘yan shekarun nan da kuma ya janyo mutuwar dubban mutane.

Masana harkar muhalli sun ce ya kamata a samar da kyakkyawan tsari domin kare irin wadannan dadaddun wuraren bauta da kuma yankin na Himalaya.

A 2021, yayin kaddamar da rukuni na wasu ayyuka, firaministan kasar Narendra Modi ya ce masu yawon bude ido da yawa zasu ziyarci jihar Uttarakhand da ke arewacin kasar a tsawon gomman shekaru masu zuwa a kan shekaru 100 da suka wuce.

Firaministan ya ce wannan na faruwa ne saboda bukatar samar da ababen more rayuwa da gwamnatin tarayya da kuma ta jihohi suka nema – karkashin jagorancin jam’iyyar Bharatiya Janata, da ta samu gagarumin goyon baya tsakanin mafi rinjayen al’ummomin Hindu na Indiya – domin ganin masu ibada sun ci gaba da zuwa wuraren ibada a Uttarakhand.

Jihar da ke cike da tsaunuka, inda ake da yawancin tsaunuka da kuma dutsar kankara, gari ne da ke tattare da wurare masu tsarki na yan kabilar Hindu, hada da garuruwan ibada na Kedarnath da Badrinath da Yamunotri da kuma Gangotri wadanda bangare ne na yankin Himalaya.

Akwai wasu wuraren bauta da dama da ake girmamawa a yankin Himalaya, hada da kogon bauta na Amarnath da na Vaishno Devi a yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi.

A tsawon Karni, ‘yan addinin Hindu sun jure tsananin sanyi da kuma hanyoyi masu hadari da tsaunin ke tattare da shi domin zuwa ibada, inda ake bude wasu na ‘yan watanni a cikin shekara.

Wurin bauta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dabun dubatar masu bauta na zuwa yin bauta a Char Dham a kowace shekara
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai masana sun ce karuwar masu ibada a cikin gomman shekaru da suka gabata – ya faru ne saboda ci gaba da aka samu na ababen more rayuwa, sai dai hakan na barazana ga muhallin yankin, da ya sha fama da girgizar kasa.

Sanya haramci ba shi ne mafita ba musamman idan dadaddun al’adu suka shigo ciki, sai dai akwai hanyoyi da dama da za a bi wajen ganin ba a musgunawa addinai ba kamar saka ka’idoji.

"Akwai ayyukan more rayuwa da ake yi a-kai-a-kai a yankin. Tun da farko, mazauna kauyukan da ke da wahalar zuwa na jira na tsawon shekaru kafin samun hanya.

A yanzu, akwai karuwa a samar da ababen more rayuwa – amma mazauna yankunan basu damu da hakan ba kamar mutane da ke cikin jihohi,’’a cewar Kiran Shinde, babban malami a jami’ar La Trobe da ke Australia, wanda ya yi aiki tukuru a bangaren yawon bude ido na addinai da kuma tsara birane.

Duk da yake gudanar da manyan tarukan addini na da wuyar gaske, kasar Indiya ta yi nasara a taruka irin na zuwa bauta a cikin kogin Kumbh Mela da ake gudanar wa a jihohi hudu, inda ake tsoma kai cikin ruwa.

Sai dai wahalhalu da ke tattare da tsaunuka da masu bauta ke zuwa na da yawa.

Yawancin ababen more rayuwa da aka gina a yankin – ciki har da aikin fadada babbar titin Char Dham - wanda masana muhalli da mazauna yankin suka kalubalanci aikin saboda yanayi na muhalli.

Ana daukar masu zuwa bauta kan dawaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana bude wannan wurin bauta na Amarnath na dan wasu watanni a shekara

Ravi Chopra, wani kwararre kan muhalli da ya jagoranci kwamiti da kotun koli ta kafa domin duba damuwa da ake nunawa kan aikin na Char Dham, ya yi murabus a watan Febrairu.

Ya rubuta a cikin wata wasika cewa "ya ji kunya’’ kan yin watsi da shawarwari da aka bayar kan aikin hanyar da wasu lauyoyi na wata babbar kotu suka yi.

"tsare-tsaren samar da ayyukan ci gaba masu dorewa musamman ma muhalli…A matsayina na mamban wannan kwamiti, akwai inda na ga an wargaza wani wuri da a da yake da muhimmanci a yankin Himalayas,’’ ya rubuta. Akwai damuwa matuka.

Kungiyar masu bincike, da suka yi bincike kan ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutum akalla 200 a jihar Uttarakhand a watan Febrairun 2021, sun bayyana a cikin wani rahoto cewa karuwar sauyin yanayi na kara yin barazana ga fadawar tsaunuka a Himalayas, wanda zai kuma kara sanya mutane cikin hadari.

Kamar sauran kasashe, Indiya ma na fuskantar matsanancin yanayi, wanda bincike ya ta’allaka faruwar hakan kan sauyin yanayi.

A farkon watan Yuli, akalla masu bauta 16 ambaliyar ruwa ta kashe bayan da mamakon ruwa ya tafi da matsugunansu kusa da wurin bauta na Amarnath.

Wani masani kan yanayi, ya fadawa manema labarai cewa ambaliyar ruwan ya faru ne sakamakon hazo hade da mamakon ruwan sama, wanda mutane basu saba gani ba.

"Ba mu da abin da za mu kwatanta ruwan sama a yankin saboda karamin wuri ne,’’ a cewar Sonam Lotus, darektan sashin kula da yanayi na yankin Jammu da Kashmir.

A 2013, garin Kedarnath ya gamu da gagarumar ambaliya – sakamakon mamakon ruwan sama – inda ruwan ya tafi da dubban mutane.

Yayin da lamarin ya kasance mai tsotsa rai a duk lokacin da aka tuna shi, hakan bai hana masu bauta ci gaba da zuwa ba domin yin bauta a bana.

Ana sa rai masu bautar za su zarta na 2019 da ya samu zuwan miliyoyin mutane, a cewar hukumomi.

Yankin Kadarnath da ambaliyar ruwa ya shafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A 2013, gagarumar ambaliya ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane da lalata dimbin gidaje a garin Kedarnath

Wadannan masu zuwa yawon bude ido, na kawowa gwamnatocin jihohi kudaden shiga da ake bukata – wanda hakan zai rage kudaden da ake zubawa.

Dr Shinde ya ce so tari ana samun gibi daga hukumomi idan aka zo batun abin da ya janyo matsala a bangaren yawon bude ido na addinai.

"Yayin da ake damawa da masu fada aji na bangaren addinai wajen kula da kudade da ake samu a wajen masu zuwa wuraren bauta, a daya bangaren ba sa daukar nauyin da ya rataya a kansu na shawo kan mummunan tasiri da hakan ke yi wa muhalli,’’ ya rubuta a wata Makala a 2018.

Yayin da ake kara samun dama, hakan ya sa mutane da dama a fadin kasar har da ketare kai ziyara zuwa wadannan wuraren bauta, masana sun ce ya kamata dukkan mutane su sake tunani kan lamarin.

"Matakai da za a dauka na karshe kan wuraren bauta, su kasance masu dan sauri ga masu zuwa ibada.

Yanzu ba zuwa wurin kadai ba, har ma da hanyoyi da za a bi na da hadarin gaske,’’ a cewar wani kwararre kan muhalli, Sreedhar Ramamurthi.

Ya kamata hukumomi su yi wa masu ruwa da tsaki magana domin ganin ci gaban tsare-tsare kan muhallai da ke dauke da wuraren bauta, a cewar Dr Shinde.

"Galibin kudaden da ake samu ba na masu zuwa ibada ba ne kadai, ana samu kuma daga limamai da ke gudanar da bukukuwa na addini ga mabiyansu zuwa kuma ga masu daukar masu ibada kan dawaki zuwa wuraren bauta.

Masu zuwa ibadar za su fi kowa sanin hanyoyi marasa hadari kan dukkan mutane,’’ a cewar Dr Shinde.

Yawancin masana sun amince cewa rage yawan masu zuwa ibada da zai dace da muhallin yana da muhimmanci.

Dadin dadawa, bullo da shirye-shiryen wayar da kai zai kuma taimaka a cewar Dr Shinde.

"Wannan sako yana da muhimmanci. Ya kamata hukumomi su samar da bayanai a-kai-a-kai ga al’umma ta hanyar tallace-tallace da sanarwa da suke fadakarwa kan hadura da ke tattare da yin tafiya zuwa wuraren bauta,’’ a cewarsa.

Yayin da ake fargabar cewa akwai matsaloli da ke tattare da sanar da sanya takunkumi kan wannan batu, Mr Modi – dan siyasar da ya fi yin fice a kasar -  zai iya daukar matakin saka takunkumin, a cewar masu zuba ido.