'Ya kamata Birtaniya ta nemi afuwa kan cinikin bayi'

Asalin hoton, BBC/ROXANNE PANTHAKI
Tauraron jarumin nan David Harewood ya ce kamata ya yi gwamnatin Birtaniya ta ba da haƙuri kan rawar da ta taka a lokacin cinikin bayi.
Jarumin ya gano cewa an bautar da kakanninsa ne a wata gonar sikari da ke Barbados.
Ya shaida wa BBC cewa gazawar gwamnatin wajen bayar da haƙuri "yana sosa wa dubban mutane a ƙasar rai waɗanda suka samo asali daga bayi".
Firaiminista Rishi Sunak a baya ya ce "yunƙurin dawo da tarihin da ya wuce ba daidai ba ne, kuma zai riƙa mayar da hannun agogo baya".
Kakannin Harewood sun yi aiki a matsayin bayi ne a gonar iyalan gidan Lascelles, waɗanda suka gina gidan Harewood a ƙarni na 18 a kusa Leeds.

Asalin hoton, ASHLEY KARRELL
Kamar duka sauran bayi, kakanin Harewood ma an matsa musu domin su ɗauki sunan da za a sauya musu wanda ya yi daidai da na Turawa.
"Dalilin da ya sa ka ji sunana Harewood ai saboda bauta ne," in ji fitaccen. Duk kuwa da cewa bai san tarihinsa ba sai a yanzu.
Lokacin da jarumin ya taɓa ziyartar gidan Harewood yana ɗan shekara 30 ya kuma yi aiki a West Yorkshire, ya yi tsammanin sunan kawai ya haɗu ne kwatsam.
"Sai daga baya a rayuwa na gano dalilin da kuma alaƙa tsakanin sunayen."
Harewood da David Lascelles waɗanda ke tafiyar da Earl Harewood , yanzu sun amince da abin da suka ji na tarihin, kuma sun amince su sanya hoton Harewood cikin jerin hotunan iyalan gidansu.
Earl Harewood ya ce: "Idan za a yi wa abin da ya gabata adalci shi ne a fara duba hanya ɗaya da za a shawo matsalar yadda bayan ya cutar da yanzu".
Hoton wanda Ashley Karrell ya zana yana cikin jerin bhotunan da suka ɓata, wanda ke nuna mabanbantan mutanen da suke da alaƙa da Harewood.
"Ba za mu iya sauya abin da ya faru ba a baya, amma za mu iya sauya abin da ke faruwa a yanzu," in iyalan gidan.
"Ina so mutane su kalli ƙoƙarin da muke yi domin mu sauya komai."
' Cin zali ne ya gina wannan gida'
David Harewood yana da fatan lokacin da masu ziyara suka zo " za su ga hoton baƙin mutum da za su iya gane wa a talabijin, za su tambaya me ya sa suka ga wannan hoton a nan, dan haka za su fahimta... duk wahalar da kakaninna suka yi ba a biya su ba, da ƙetar da aka yi musu... su ne suka taimaka aka gina wannan gida".
Yadda ake yunƙurin tattauna laifukan da aka tafka lokacin bautar da mutane abu ne da ake tattaunawa yanzu. Barbados ce ke jan ragamar yadda za a biya mutane diyya, wanda si kansa HArewood ke goyon baya.
Magajin Firaiministan ƙarnin na 19 William Gladstone ya je Guyana, iyalai na baya-bayan nan da suka je bayar da haƙuri ga 'yan uwansu da matsalar cinikin bayi ta shafa.

Asalin hoton, SCIENCE PHOTO LIBRARY
Kamar dai fitaccen jarumin, suma iyalan gidan na fatan gwamnatin Birtaniya ta bayar da hakuri a hukumance.
"Ina ganin wanan wani abu ne da ya kamata ya faru a matakin ƙasa... a wannan lokacin da muke da firaiminista mai rauni alamu na nuna babu wani abu da zai faru, wanda wannan abin takaici ne."
A farkon wannan shekarar, Mista Sunak ya ce " kamata ya yi a mayar da hankali kan fahimtar tarihinmu da duka ɓangarorinsa, maimakon ƙaurace masa, a yanzu na yi amannar muna da al'ummar da ta haɗe kowa kuma da mutane masu haƙuri da juna daga ɓangarori daba-daban.
Sarakunan earl na yanzu ba su damu da cewa waɗanda abin ya rutsa da su ba su yi haƙuri.
"Ni ban damu da in hakan ba, tun da ba ni ne na aikata laifin ba," ya ƙara da cewa, iyalan masarautarsu sun kashe fan miliyan guda kan ayyukan ci gaba da waɗanda aka bautar.

Asalin hoton, HAREWOOD HOUSE TRUST
Idn Harewood ya nemi a ba shi haƙuri, babu shakka zai samu guda kai tsaye daga gare ni," in ji shi.
Akuyoyi da alade da tinkiyoyi da kuma shanu na cikin jerin sunayen waɗanda aka bautar.
Yayin da aka haramta sayar da bayi, sai da aka biya masu bayi diyya. tsakanin shekarun 1835 da kuma 1836, Hanry Lascelles mai sarautar Earl na Harewood na biyu ya samu fan 26,307 kuɗin bayi 1,277 - a yau darajar kuɗin ta kai fan milyan 2.6.
Amma su bayin ba a basu komai ba daga cikin kuɗin.

Asalin hoton, HAREWOOD HOUSE/BORTHWICK INSTITUTE OF ARCHIVES
Wannan rashin adalci da aka yi wa bayin ba ya nufin komai ga David Harewood. ya yi ta fama da samun kudin diyyar iyalansu ne da suke cikin wannan lamari.
Ya shaida min yadda yake ji a lokacin, "yana jin ba daɗi sosai" idan yana zaune a gida.
"Akwai wani lokaci da zan ji kamar kamar na yi ihu saboda abin da nake ji yana ƙona ni ta cikin jikina... Amma ni da kaina ban san me hakan yake nufi ba da ni."

Asalin hoton, ALAMAY
"Duk lokacin da wani baƙin mutum ya tashi zai yi magana kan abin da aka yi lokacin cinikin bayi, sai a riƙa yi wa lamarin kallon zagon ƙasa ga Birtaniya," in ji shi.
A littafin da ya rubuta kan rayuwarsa ya ce, Watakila ne ba ɗan nan ba ne, in ji Harewood a matsayin wani matashin yaron da ya fito daga Birmingham wanda burinsa shi ne ya zama cikin fitattun Hollywood".
Ya kasance kan dandali da kuma majigi a matsayin Martin Luther King da kuma Nelson Mandela a 1997, shi ne baki ɗaya tilo da ya taba taka rawa a ɗakin wasa na Othello.
Yanzu akwai zanen hotonsa a ɗaya daga cikin ɗakin zanen da ke ƙasar. "Ina ganin magabatanmu za su ji daɗi."












