Kafar Man City ɗaya ta fice daga Champions League

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta yi rashin nasara da ci 3-2 a wasan farko na cike gurbi a Champions League da suka fafata a Etihad ranar Talata.

City ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Erling Haaland a minti na 19 da fara wasan, kuma haka suka je hutu ana cin Real Madrid 1-0.

Bayan da wasa ya nutsa a zagaye na biyu ne Real ta farke ta hannun Kylian Mbappe.

Haaland shi ne ya kara na biyu a ragar Real Madrid a bugun fenariti, amma kuma Brahim Díaz ya farke wa Real saura minti huɗu a tashi daga karawar.

Sai dai daf da za a tashi ƙungiyar Sifaniya ta ci na uku ta hannun Jude Bellingham.

Wannan shi ne wasa na 13 da suka kece raini a tsakaninsu, City da Real kowacce ta yi nasara huɗu da kuma canjaras biyar a wasannin zakarun Turai.

City ta samu matakin cike gurbin gasar, bayan karewa ta 22 a rukuni, sakamakon cin wasa uku da canjaras biyu aka doke ta karawa uku.

Ita kuwa Real Madrid ta 11 ta yi a kan teburi, wadda ta yi nasara biyar aka doke ta wasa uku.

Ranar Laraba 19 ga watan Fabrairu, Real Madrid za ta karɓi bakuncin City a wasa na biyu na cike gurbi a Champions League a Santiago Bernabeu.

Duk wadda ta yi nasara a tsakani, za a haɗa ta da daya daga waɗanda suka kai zagayen gaba kai tsaye tun farko, domin fafatawa a zagayen ƴan 16.