Har yanzu ina sa ran lashe Premier 2018 - Mourinho

A

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho ya yi iƙirarin ba zai yanke ƙauna ba ta dawo masa da kofin Premier 2018, wanda har yanzu ake yi wa Manchester City shari'a cewa ba ta cancanci cin kofin ba.

United ta ƙare a matsayi na biyu kakar 2017-18, wadda ita ce kakar da Mourinho ya bar Old Trafford.

City wadda tun daga lokacin ta ci Premier sau huɗu a jere, ana zarginta da karya dokar kashe kudi tsakanin 2009 zuwa da 18.

City ta musanta tuhume-tuhume 155 da ake yi mata, kuma ana sa ran sakamakon binciken ya fito a farkon 2025.

Idan aka samu ƙungiyar da laifi za a kwace kofin da ta ci a bai wa ta biyu a wannan lokacin.

An tambayi Mourinho kan tsohuwar ƙungiyarsa da za ta fafata da Fenerbache a Europa a Istambu a ranar

"Kamar yadda kuka sani mun ci Europa a 2017, mun zo na biyu a Premier na biyu a 2018," in ji shi.

"Ina ganin har yanzu muna da damar lashe wannan kofin watakila za a hukunta Man City ta hanyar cire mata maki, sai mu ci kofi su biyani kuɗaɗena su bani sarƙa."