Jota ba zai buga wasan Liverpool da Arsenal ba

Diogo Jota

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Liverpool Arne Slot ya ce ɗan wasan gaba Diogo Jota ba zai buga wasan Premier da za su yi da Arsenal ranar Lahadi ba.

An maye gurbin Jota ne a nasarar da suka yi da Chelsea a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya samu rauni a kirji lokacin da suka yi karo da ɗan wasan baya na Blues Tosin Adarabioyo.

Ɗan wasan na Portugal bai buga wasan da Liverpool ta doke RB Leipzig a gasar cin kofin zakarun Turai ba a ranar Laraba ba kuma ba zai buga wasan da za su kara da Gunners ba a ranar Lahadi, tare da ɗan wasan gefe Federico Chiesa.

Mai tsaron raga Alisson Becker ya ci gaba da jinya sakamakon raunin da ya ji a wasan da suka yi nasara a Crystal Palace ranar 5 ga watan Oktoba kuma ana sa ran zai dawo a tsakiyar watan Nuwamba.

Liverpool ce ke kan gaba a teburin gasar Firimiya kafin wasannin wanna makon kuma tana da tazarar maki huɗu a kan Gunners da ke matsayi na uku, wanda Slot ya ce sun yi wa Reds nisa cikin shekaru biyu da suka gabata.