Me ayyana hawan dabar Kano a matsayin muhimmiyar al'ada ta UNESCO ke nufi?

Asalin hoton, Mai Katanga Photography
Hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta ayyana hawan dabar jihar Kano a matsayin ɗaya daga cikin al'adu masu muhimmanci a duniya.
UNESCO ta ayyana haka ne ranar Alhamis, inda ta ce hawan dabar da aka saba yi a lokutan bukukuwan sallah, na da muhimmancin gaske a jerin al'adu da take alfahari da su.
Hawan dabar dai da aka soma tun cikin ƙarni na 15, na nuna yadda Sarki da dubban mahaya dawaki ke zagayen gari tare da rakiyar mawaƙa a kan titunan birnin na Kano.
Yawanci ana gudanara da wannan al'ada ce sau biyu a shekara, wato lokacin bikin ƙarama da kuma babbar sallah.
Birane da dama a arewacin Najeriya na gudanar da hawan daba a lokutan na bikin sallah.
Sai dai wanda ya fi girma shi ne na Kano, birni mafi girma a arewacin Najeriya.
"Hawan daba na da armashin gaske, ga mutunci da kuma haɗin kai, in ji Hajo Sani, wadda ta wakilci Najeriya a taron UNESCO karo na 19, wanda aka yi a Asuncion, babban birnin Paraguay.
"Bikin al'ada ne mai girman gaske wanda yake haɗa kabilu daban-daban, ciki har da Hausawa da Fulani da Larabawa da Nufaawa da Yarabawa da kuma Buzaye, inda suke taruwa a matsayin al'umma ɗaya," in ji Hajo.
Sarki dai wani babban jigo ne a ƙasar Hausa, inda a kowane lokaci yake samun rakiyar fadawa da masu kula da shi da kuma manyan muƙarrabai a lokacin hawan dabar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sarki tare da tawagarsa na zagaye a faɗin anguwanni a birnin Kano, yayin da al'ummarsa ke gaisuwar ban-girma da kuma nuna goyon baya, a cewar shafin intanet na UNESCO.
Duk da cewa sarakunan gargajiya ba su da iko a kundin tsarin mulki, amma suna da muhimmancin gaske a al'adance waɗanda al'umma ke girmamawa da kuma ke da tasirin gaske musamman a jiha irin Kano.
Ƴansandan jihar Kano sun hana hawan daba a lokacin bikin babbar sallah a watan Yunin 2024 kan dalilai na tsaro, bayan da zaman tankiya ya sanadiyyar rikici na sarauta.
"Hawan daba dai wani ɓangare ne da ke samar da ayyukan yi, da kuma kyautatuwar tattalin arziki tsakanin al'ummomi", in ji Hajo Sani.
Ta ƙara da cewa "bikin hawan daba ya shahara har ta kai ga jihohi da dama a arewacin Najeriya na gudanar da shi a yanzu, ciki har da babban birnin tarayya Abuja".
Hawan daba ya bi sahun sauran bukukuwan al'ada a Najeriya wajen shiga jerin al'adu da UNESCO ta ayyana a matsayin masu muhimmanci, ciki har da bikin Sukur da ake yi jihar Adamawa da kuma wani bikin al'adar a jihar Osun da ke kudancin Najeriya.










