Yadda aka yi hawan Daushe a Kano

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Yadda aka yi hawan Daushe a Kano
An wallafa

Mai marataba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi hawan Daushe da yammacin ranar Alhamis tare da hakimansa.

Hawan Daushe zagaye ne da mai martaba Sarkin Kano ke yi tare da hakimansa nasa a kan dawakai cikin ado da farin ciki, inda mutanen gari kuma ke kai gaisuwa da caffa.

Tawagar na farawa ne daga kofar arewa ko kuma kofar kwaru zuwa kofar kudu na masarautar ta Kano, inda ake sukuwa a gaban manyan baki daga gida da wajen Najeriya, kafin daga bisani Sarki ya yi ban bankwana ya shiga gida.

Jerin haye-hayen da ake yi a Kano:

  • Hawan Sallah
  • Hawan Daushe
  • Hawan Nassarawa
  • hawan fanisau
  • Hawan Dorayi