Man United ta kammala ɗaukar Dorgu daga Lecce

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta kammala ɗaukar mai tsaron bayan tawagar Denmark, Patrick Dorgu daga Lecce kan yarjejeniyar kaka biyar da rabi.

Ƙudin da aka yi cinikin ɗan wasan mai shekara 20-ya kai £25m da karin £4.1m na tsarabe-tsarabe.

Dorgu ya buga wa Lecce wasa 57 tun lokacin da ya fara taka mata leda a bara, bayan da ya koma ƙungiyar a matashi a 2022.

An hakura da batun cewar Tyrell Malacia, mai shekara 25 da zai koma Benfica ta Portugal.

An tsara cewar Marcus Rashford zai je a auna koshin lafiyarsa kafin a ruffe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo ranar Litinin, wanda zai koma wasannin aro a Aston Villa.

Rabonda Rashford ya yi wa United wasa tun ajiye shi da koci, Ruben Amorim ya yi a karawa da Manchester City ranar 12 ga watan Disamba.

An gabatar da Patrick Dorgu da Ayden Heaven a gaban magoya baya, kafin take wasan Premier League tsakanin United da Crystal Palace ranar Lahadi.

Dorgu shi ne na biyu da United ta ɗauka a Janairun nan, bayan ɗan wasan tawagar Ingila mai shekara 19, Ayden Heaven daga Arsenal.

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images