An ci Man United a karon farko a wasan waje a Premier a bana

Erik ten Hag

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta yi rashin nasara a karon farko a wasan waje a Premier League a bana, inda Brighton ta doke ta 2-1 ranar Asabar.

Danny Welbeck ne ya fara ci wa Brighton ƙwallo a minti na 32, kuma na 100 da ya zura a raga a dukkan fafatawa a ƙungiyar.

Welbeck, tsohon ɗan wasan United ya ci ƙungiyar Old Trafford ƙwallo na shida kenan, wanda ya zura bakwai a ragar West Ham, ita ce ya fi zura wa ƙwallaye.

Bayan da suka yi hutu ne suka koma zagaye na biyu United ta farke ta hannun Amad Diallo, bayan da ya samu tamaula ta hannun Noussair Mazraoui.

Kenan United ta ci ƙwallo ta hannun ɗan Afirka, kuma takwaransa daga nahiyar ne ya ba shi ƙwallon.

Daf da za a tashi daga wasan Brighton ta kara na biyu ta hannun Joao Pedro, wanda hakan ya sa ƙungiyar ta haɗa makin da take bukata.

Tun daga 20222/23, United ta yi rashin nasara a lokacin daf a tashi wasan Premier League ko dai a minti na 90 ko fiye da haka har sau shida.

Ranar 17 ga watan Agusta, Brighton ta je ta ci Everton 3-0 a Goodison Park, ita kuwa United ta yi nasara a kan Fulham 1-0 a Old Trafford ranar Juma'a 16 ga watan Agusta.

Ranar Talata 27 ga watan Agusta, Brighton za ta karbi bakuncin Crawley, domin karawa a gasar League Cup daga baya ta je Arsenal ranar Asabar 31 ga watan Agusta a Premier League.

Ita kuwa Manchester United za ta karɓi bakuncin Liverpool a wasan mako na uku ranar Lahadi 1 ga watan Satumba a Old Trafford.