Yadda Barcelona ta samu nasara a kan Las Palmas

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwallon da ɗan wasan Barcelona, Ilkay Gundogan da ya ci a bugun fanaret ita ce ta zama raba gardama kuma ta bai wa kulob din nasara a kan Las Palmas.
Las Palmas dai ya sauya ɗan wasansa Daley Sinkgraven bayan tunkude tsohon dan wasan tsakiya na Macnhester City din a lokacin da yake gab da jefa kwallo a ragar Las Palmas da kansa, abin da ya janyo masa jan kati.
Las Palmas dai ba su ji dadin fanaretin da jan kati ba.
Kocin Barcelona, Xavi Hernadez ya ce " Akwai kaɗuwa a koyaushe. Akwai tsoro, kowa na son samun nasara. Idan ka yi min batun fanaret, abu ne da zan iya fahimta.
"Mun yi nasara daga ƙarshe ta hanyar fanaret. Na gane cewa Kirian, amma dai ture ne kuma ya zama fanaret."
Yanzu haka wannan nasarar ta bai wa Barcelona jumullar maki 41 a wasanni 19 da ta taka a gasar La Liga.
Kuma waɗannan makin ne mafi yawa a karo na biyu da kulob din ya taba samu a wannan zangon wasan, a kakar wasanni biyar da suka gabata.
Barcelona ce yanzu ta uku a teburin gasar ta La Liga, inda take biyewa Real Madrid da tsiran maki bakwai.Ita kuwa Las Palmas ta kasance ta 10 a teburin gasar ta La Liga, bayan fuskantar rashin nasara a wasanni biyu da ta taka a jere.










