Sporting da Arsenal za su yi wasa na biyar a tsakaninsu

Asalin hoton, PA Media
Sporting Lisbon da Arsenal za su kara a wasan farko zagayen 'yan 16 a Europa League a kakar nan.
Wannan shine wasa na biyar da za su kece raini a tsakaninsu, inda Arsenal ta yi nasara a biyu da canjaras biyu.
Arsenal ta kawo wannan matakin, bayan jan ragamar rukunin farko da maki 15, ita kuwa Sporting daga Champions League ta koma buga Europa.
Kungiyar Portugal ta yi nasara a kan FC Midtjylland a fafatawar da suka yi gida da waje da cin 5-1 a wasan cike gurbin shiga Europa League.
Kocin Arsenal, Mikel Arteta bai fayyace ko Gabriel Jesus zai yi fafatawar ba, wanda ya yi atisaye a Gunners ranar Laraba.
Rabon da ya taka leda tun cikin Disamba, amma yanzu ya murmure har ya yi atisaye kafin Gunners ta wuce Portugal.
Jesus tsohon dan wasan Manchester City ya ci kwallo biyar a karawar Arsenal ya bayar da shida aka zura a raga a Premier League a kakar nan.
Arsenal ba ta taba daukar Europa League ba, ita kuwa Sporting tana fatan lashe kofin a karon farko.
Arsenal tana matakin farko a kan teburin Premier League, kofin da take fatan dauka a karon farko tun kusan bayan shekara 20.
Wasa hudu da aka kara tsakanin Sporting da Arsenal
2018/2019 Europa League
- Arsenal 0 - 0 Sporting
- Sporting 0 - 1 Arsenal
1969/1970 Fairs Cup
- Arsenal 3 - 0 Sporting
- Sporting 0 - 0 Arsenal










