Emile Smith Rowe zai yi jinyar watanni bayan yi masa tiyata

An wallafa

Dan wasan tsakiya na Arsenal Emile Smith Rowe zai yi jinyar watanni bayan tiyatar da aka yi masa a tsakanin jinyoyinsa.

Dan wasan zai koma atisaye ne a watan Disamba mai zuwa.

Wasa hudu dan wasan ya buga a wannan kakar, kuma duka ya shiga a canji ne.

A wasan karshe da ya buga wanda suka yi da Manchester United, ya samu "mummunan koma baya".

"A yan watannin nan Emile Smith Rowe na fuskantar rashin nutsuwa a jinyarsa, wanda hakan ya sa ya rage yawan atisaye da buga wasanni," in ji Arsenal.

"Bayan wannan koma baya da ya samu a wasanmu na Premier da Manchester United a Old Trafford a ranar 4 ga watan Satumba, amma bayan tattaunawa da tuntubar likitocinmu, an yi wa Emile tiyata domin gyara masa raunin da ya ji a cinyoyinsa.

"An yi masa wannan tiyatar ne cikin nasara kuma a Landan a kwanakin da suka gabata kuma ana ci gaba da yi masa bayanai da za su kwantar masa da hankali.

"Muna sa ran Emile zai dawo atisaye a watan Disamba."