Emile Smith Rowe zai yi jinyar watanni bayan yi masa tiyata

Smith ya fara buga wasa ne a Ingila a wasan da ta ci Albania a watan Nuwamban 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Smith ya fara buga wasa ne a Ingila a wasan da ta ci Albania a watan Nuwamban 2021
An wallafa

Dan wasan tsakiya na Arsenal Emile Smith Rowe zai yi jinyar watanni bayan tiyatar da aka yi masa a tsakanin jinyoyinsa.

Dan wasan zai koma atisaye ne a watan Disamba mai zuwa.

Wasa hudu dan wasan ya buga a wannan kakar, kuma duka ya shiga a canji ne.

A wasan karshe da ya buga wanda suka yi da Manchester United, ya samu "mummunan koma baya".

"A yan watannin nan Emile Smith Rowe na fuskantar rashin nutsuwa a jinyarsa, wanda hakan ya sa ya rage yawan atisaye da buga wasanni," in ji Arsenal.

"Bayan wannan koma baya da ya samu a wasanmu na Premier da Manchester United a Old Trafford a ranar 4 ga watan Satumba, amma bayan tattaunawa da tuntubar likitocinmu, an yi wa Emile tiyata domin gyara masa raunin da ya ji a cinyoyinsa.

"An yi masa wannan tiyatar ne cikin nasara kuma a Landan a kwanakin da suka gabata kuma ana ci gaba da yi masa bayanai da za su kwantar masa da hankali.

"Muna sa ran Emile zai dawo atisaye a watan Disamba."