Wane hali Iran za ta shiga bayan rasuwar Shugaba Raisi?

President Ebrahim Raisi

Asalin hoton, EPA

    • Marubuci, Lyse Doucet
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief international correspondent
  • An wallafa

Ebrahim Raisi ya kasance ɗaya daga cikin na gaba-gaba a farfajiyar mulkin Iran kuma shi ne aka yi zaton zai ɗare ƙololuwar mulkin kasar a nan gaba, wato shi ake sa ran zai gaji babban jagoran addinin ƙasar.

Sai dai mutum na nashi Allah Yana Nashi.

Mutuwarsa a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu ranar Lahadi, a yanzu ta kawo ƙarshen duk wasu raɗe-raɗi da ake yi a kansa na cewa zai gaji jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, mai shekara 85, wanda yanayin lafiyarsa shi ma ya kasance wani abu da ke ɗaukar hankali sosai.

Wannan mutuwa ta ban-tausayi da shugaban na Iran mai ra'ayin riƙau ya yi ba a tsammanin za ta haifar da wani gagarumin sauyi ko cikas ga manunfofin kasar.

To amma za ta zama wani zakaran-gwajin-dafi ga tsarin tafiyar da mulkin kasar wanda masu ra'ayin riƙau suka kankane komai da ko'ina a mulki, kama daga bangaren zababbu ko kuma wadanda ba zababbu ba.

“Tsarin zai yi matukar nuni ga mutuwarsa da kuma yadda za a bi matakan kundin tsarin mulki, yayin da za a nemi wani sabon shugaban da zai ci gaba da bin aƙida da manufar hadin kai da biyayya ga Khamenei,” in ji Dakta Sanam Vakil, darakta kan harkokin Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Arewa a cibiyar kwararru ta Chatham House, da ke Landan.

Abokan hamayyar Raisi babu shakka za su yi farin ciki da gushewar tsohon mai gabatar da karar wanda ake zargi da taka babbar rawa wajen aiwatar da hukuncin kisa a kan fursunonin siyasa da dama a shekarun 1980, abin da ya musanta; za su yi fatan cewa kawo karshen gwamnatinsa zai hazarta kawo karshen wannan mulkin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ga masu mulkin kasar Iran masu ra'ayin rikau jana'izar kasa da za a yi wa marigayin za ta kasance wani lokaci da za su dauki hankalin jama'a tare da sosa ran al'umma da aikawa da sako na ci gaba da manufofinsu.

Sun san cewa duniya ta zuba ido tana gani.

“Ga fahimta da bayanan kasashen yamma tun shekaru 40 baya, suke ganin ya kamata Iran ta rushe," in ji Farfesa Mohammed Marandi na jami'ar Tehran a hirarsa da BBC.

"To amma abin mamaki har yanzu tana nan kuma ina hasashen za ta ci gaba da kasancewa har zuwa wasu shekaru nan gaba.”

Wani mukami mai muhimmancin gaske da kuma ya zama wajibi a cike gurbinsa shi ne na kujerar da marigayin yake rike da ita a majalisar manyan malamai - wato majalisar da ke zaben sabon babban jagoran addinin kasar, a duk lokacin da mai rike da wannan mukami mafi girma da muhimmanci a kasar ya rasu.

“Raisi zai iya zama magajin babban jagoran addinin, saboda shi ma Khamenei ya hau wannan mukami ne lokacin yana da karancin shekaru, da biyayya da kuma bin akidar tsarin sau da kafa,”in ji Dr Vakil, a game da yadda za a cike wannan gurbi, inda ake ambato sunaye da yawa ciki har da sunan dan jagoran addinin, Mojtaba Khamenei.

Daman tun kafin a tabbatar da mutuwar Raisi a hukumance babban jagoran addinin ya fito fili ya gaya wa ƴan kasar cewa kada su tayar da hankalinsu babu abin da zai tsaya na tafiyar da harkokin kasar.

Babban kalubale na farko da ke gaba a yanzu shi ne na shirya zaben sabon shugaban kasa na wuri domin cike gurbin.

Yanzu dai an mika mulki ga mataimakin shugaban kasa Mohammad Mokhber; to amma dole ne a gudanar da sabon zabe cikin kwana 50.

Masu zabe a kasar za su sake samun kansu ne a wannan yanayi na sake komawa ga runfunan zabe bayan 'yan watanni da gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a a watan Maris, zaben da bai samu halartar jama'a ba sosai, a kasar da a da take tunkaho da yadda mutane ke hankoron yin zabe.

Zabukan da aka yi a baya-bayan nan ciki har da na 2021 wanda ya kawo Raisi kan kujerar shugabancin, sun gamu da kalubale na yadda hukumar zabe ta hana masu matsakaicin ra'ayi da masu neman kawo sauyi shiga takara.

“Zaben shugaban kasa na wuri ka iya bai wa Khamenei da sauran manyan jagororin kasar damar sauya ra'ayin masu zaben ta yadda za su dawo musu da sha'awar kada kuri'a,” in ji Mohammad Ali Shabani, editan jaridar intanet ta Amwaj.media da ke Landan.

Ya kara da cewa “To amma abin takaicin shi ne zuwa yanzu babu wata alama daga shugabannin ta daukar wannan mataki.”

Bayanan bidiyo, Shugaban ƙasar Iran jim kaɗan kafin hatsarin jirgin da ya yi ajalinsa

To amma hatta a tsakanin sa'o'i ko takwarorin Raisi, ba wani da yake a fili da za a iya cewa shi ne zai maye gurbinsa.

“Akwai bangarori daban-daban hatta a cikin wannan rukuni na masu ra'ayin rikau wadanda suka fi tsattsauran ra'ayi da kuma wadanda ake ganin masu sassauci ne,” kamar yadda Hamidreza Azizi, na cibiyar masana ta SWP, da ke Berlin, a Jamus.

Masanin na ganin wannan zai kara tsaurara gwagwarmayar neman mukami a sabuwar majalisar da kuma sauran matakan gwamnati na kasa.

Duk wanda ya hau kujerar ta Raisi to zai gaji tsari na abubuwa da dama da ba zai iya sauya su ba sai dai ya bi yadda tsarin da ya gada yake, sannan kuma zai kasance da iko takaitacce.

Ikon zartar da hukunci na karshe a Iran yana hannun babban jagoran addini na kasar.

Al'amuran da suka shafi manufa kan kasashen waje a yankin iko ne na rundunar juyin juya hali ta kasar ta Iran wato (IRGC) wadda ke da matukar iko a hannunta.

Misali, shugaban kasar bai bayar da wani umarni ba watannin da suka gabata, lokacin da zaman tankiya ya karu tsakaninta da babbar abokiyar fadanta Isra'ila, a kan mummunan yakin Gaza.

Yakin ya haifar da yanayi na neman ramuwar gayya a manyan biranen kasashen yankin da dama musamman Tehran, a kan yuwuwar fadadar rikicin .

To amma yayin da yake tafiyar da harkokinta na yau da kullum , 'yan Iran na fama da matsalar rayuwa, wadda ke da alaka da takukumin da kasashen duniya suka sanya mata, da kuma rashawa.

Tashin farashin kaya ya karu zuwa sama da kashi 40 cikin dari - kuma darajar kudin kasar ta fadi sosai.

Haka kuma a karkashin shugabancin Raisi, Iran ta yi fama da zanga-zanga ta gama-gari wadda ta barke a sanadiyyar mutuwar matashiya Mahsa Amini, mai shekara 22, a hannun 'yan Hisbah a watan Satumba na 2022, wadda aka tsare bisa zargin kin rufe kanta da mayafi ko hijabi.

'Yan makonni kafin barkewar zanga-zangar Raisi ya bayar da umarnin tsaurara dokar tufafi ta kasar, wadda ta tilasta wa mata su sanya tufafi na kamala ciki har da rufe kansu.

Zanga-zangar wadda matasan mata suka jagoranta, a kan tsauraran dokokin da suka shafi rayuwarsu, ta mayar da hankali ne a kan suka da nuna fushi ga ainahin mai rike da iko na kasar wato babban jagoran addini da kuma tsarin tafiyar da mulkin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun ce an kashe ɗaruruwan mutane a yayin murkushe zanga-zangar tare kuma da tsare dubbai.

“Kasancewar an zabe shi da kuri'u mafiya karanci a tarihin zaben shugaban Iran, Raisi ya kasance ba shi da farin jini da iko kamar na wanda ya gada, Rouhani,“ in ji Shabani da yake kwatanta shi da Rouhani, mai ra'ayin kawo sauyi, wanda farin jininsa ya karu saboda muhimmiyar yarjejeniyar nukiliya ta 2015, wadda ta rushe lokacin da Shugaba Trump, ya fitar da Amurka daga cikinta bayan shekara uku.

Tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba tsakanin bangarorin biyu - tsakanin gwamnatin Shugaba Biden da wakilan gwamnatin Raisi ba ta yi wata nasara ba.

Hossein Amir-Abdollahian

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hatsarin ya kuma yi sanadin mutuwar ministan harkokin ƙasashen waje na ƙasar Hossein Amir-Abdollahian

Hadarin jirgin saman mai saukar ungulu, ya hada da ran ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen gabatar da halin da Tehran ke ciki ga duniya domin sama mata sassauci a kan takunkumin da aka sanya wa kasar.

A lokacin tattaunawar diflomasiyya ta gaggawa a kan yakin Ira'ila a Gaza, yawanci shi ne yake magana ta waya da kuma a wajen taro daga bangaren Iran da kawayenta, da kuma taro da Larabawa da kuma ministocin waje na kasashen yamma, inda ake ta kokarin kwantar da hankali.

“Yana da muhimmanci sosai wajen isar da sako,” in ji wani babban jami'in diflomasiyya na yamma. “To amma abin ya na da wuyar sha'ani saboda, ikon zartarwa ba a hannun ma'aikatar harkokin waje yake ba.”

“Mutuwar shugaban kasa ta kwatsam galibi tana da matsala, hasali ma kuma da ake ganinsa a matsayin wanda zai iya zama magajin babban jagoran addinin kasar, ba shi da cikakken goyon baya na siyasa da kuma fitacciyar manufa ta siyasa,” in ji masani Esfandyar Batmanghelidj, shugaban cibiyar nazari ta Bourse and Bazaar.

“To amma jagororin siyasar da suka sanya aka zabe shi, za su sake shiri su kuma ci gaba duk da rashinsa.”