Wasu batutuwan da suka shafi Premier League ta bana

An wallafa

Ranar Juma'a za a fara gasar Premier League ta bana, inda za a kara tsakanin Burnley da Manchester City.

City ce ke rike da kofin bara, wanda ta dauka har da FA Cup da Champions League.

Ga jerin batuwan da suka shafi Premier League:

Kofi Uku a jere: - Manchester City ta dauki Premier League uku a jere ta yi kan-kan-kan da Manchester United da kuma lashe biyar a kaka shida.

Maki 89 - Makin da Man City ta hada a bara da tazarar biyar tsakaninta da Arsenal ta biyu.

Yawan ƙwallayen da ɗan wasa ya zura: 36 - Yawan kwallayen da Erling Haaland ya ci kenan, da suka ba shi damar lashe takalmin zinare da ake kira Golden Boot.

Yawan kofunan da wata kungiya ta ɗauka 13 - Manchester United ce kan gaba a ɗaukar kofin Premier, inda take da 13 da tazarar shida tsakaninta da City, abokiyar hamayya.

Sauran kungiyoyin da suka dauki Premier League Chelsea (biyar), Arsenal (uku), Blackburn da Leicester da Liverpool (kowacce daidai).

Yawan kofin da koci ya ɗauka 13 - Sir Alex Ferguson kan gaba wajen lashe kofin Premier wanda ke da 13, sai Pep Guardiola mai biyar da ke binsa a baya.

Ƙungiyoyin da suka buga gasar a tarihi 51 - Sabuwar kungiya Luton, ita ce kungiya ta 51 da za ta buga Premier League ta kakar nan.

A bara karo na hudu dukkan kungiyoyin da suka hau Premier League da ya hada da Bournemouth da Fulham da Nottingham Forest - ba su fadi daga wasannin ba za a buga kakar bana da su.

Maki mafi yawa da kungiya ta haɗa a gasar: 100 - Man City ce ta haɗa maki 100 mafi yawa a tarihinh gasar, ind ta samu maki 100 a kakar 2017-18, sannan kuma ta zura ƙwallo 106 a raga a kakar da ta wuce.

Yawan ƙwallon da aka ci a wasa: 9-0 Yawan kwallayen da aka ci a wasa daya a Premier League a tarihi shi ne wanda Liverpool ta ci Bournemouth.

Yawan wasannin da ɗan ƙwallo ya buga: 653 ɗan wasan da ya fi kowa buga wasanni a gasar shi ne Gareth Barry, sai James Milner mai 619.

Kaka ta 32 - Wannan ce gasa ta 32 a kakar Premier League tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.

Sau shida ana fara gasar ranar Juma'a - Wannan ce kaka ta shida da ake fara wasan Premier League da karawa daya ranar Juma'a.