Arteta na tausayin Potter kan halin da ya tsinci kansa a Chelsea

An wallafa

Mikel Arteta ya ce yana jin tausayin Graham Potter kan tsaka mai wuya da yake fuskanta a Chelsea.

Kungiyar Stamford Bridge tana ta 10 a teburin Premier League, bayan da Tottenham ta doke ta ranar Lahadi.

Kenan Arteta, wanda Arsenal ke mataki na daya a teburin Premier, ya bai wa Potter tazarar maki 26.

Wasa tara Potter ya yi nasara daga 26 da ya ja ragama a Chelsea a dukkan fafatawa, tun bayan da ya maye gurbin Thomas Tuchel a Satumba.

Tun kan Chelsea ta kara da Tottenham, tsohon kociyan Brighton ya sanar cewar ya karbi sakon barazanar kisa har da iyalansa ta kafar intanaet.

Arteta ya ce ya san matsin da Potter ke fuskanta da halin da yake ciki da rashin kwanciyar hankali, abu ne da ya kamata a tausaya masa ne.

Arteta, wanda Arsenal za ta ziyarci Everton ranar Laraba ya fuskanci irin wannan matsin a kakar farko a Gunners.

Magoya baya sun yi ta yi masa ihu da kiraye-kirayen a kore shi daga Arsenal, da cewar aikin ya yi masa girma, yanzu ya zama abin jinjina a koda yaushe.

Arteta ya ce tamaula ta wannan zamani an alakantata da samun sakamako ta wajen lashe wasa da cin kwallaye.

Koci ba shine ke buga tamaula ba, illa zai yi tunani da zabar 'yan wasan da suka dace da bin umarnin da ya basu na ganin yadda za a yi nasara a wasanni.

Arteta ya kara da cewar aiki iri daya suke gudanarwa, kuma gasar Premier tana tattare da kalubale da yawa, ina fatan zai samu damar kamo bakin zaren nan gaba.

Potter kwararre ne ya kuma nuna kansa a Brighton a tsawon aikin da ya yi a kungiyar, sai an kara hakuri kafin abubuwa su komai daidai.

Sai dai har yanzu mahukuntan Chelsea, sun ce suna goyon bayan kungiyar, shine zai komara da kungiyar kan ganiya.

Idan Arsenal ta ci Everton ranar Laraba za ta bai wa Manchester City tazarar maki biyar a teburin Premier League.