Abubuwan da Majalisar ƙasa ta buƙaci CBN ya yi kan matsalar sauya fasalin takardun Naira

CBN

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.
An wallafa

Majalisar magabata ta kasa a Najeriya wato Council of State, ta kammala wani taron gaggawa a fadar shugaban kasar da ke Abuja inda ta bukaci babban bankin kasar, CBN ya samar da karin sababbin takardun kudi domin amfanin al'ummar kasar.

A cewar majalisar, idan sababbin kudin ba za su samu ba, to CBN ya koma bai wa jama'a tsofafun takardun kudin.

Majalisar - wadda ke karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari - ta kira taron ne domin tattaunawa ka halin da kasar ke ciki a yanzu da ta ke tunkarar babban zabe.

Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.

Ta kuma ce duk da matsalolin da ake fuskanta, tana goyon bayan tsarin babban bankin na sake fasalin naira.

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku wanda ya yi wa manema labarai karin bayani ya ce, "An shawarci CBN ya samar da kudi ga jama'a sannan kuma a sake fito da tsofaffin kudi domin kawo karshen wahalar da jama'a ke fuskanta."

A waje daya kuma shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC Mahmood Yakubu, ya yi wa majalisar bayanai game da shirye-shiryen babban zaben kasar inda ya nuna cewa hukumar ta kammala shirin gudanar da zabukan da za a yi daga karshen wannan watan.

Shi ma babban sufeto-janar na 'yan sandan kasar Usman Alkali, ya yi wa majalisar bayanai game da irin matakan tsaro da suke shirin dauka a lokacin zaben.

Gwamnatin Ganduje ta shigar da kara kan canjin kudi

CBN

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnatin Jihar kano ta kai gwamnatin tarayyar Najeriya, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari kara a Kotun Kolin kasar akan sauyin fasalin wasu daga cikin manyan kudin kasar na naira 200 da 500 da 1,000.

A karar, wadda babban lauyan gwamnatin jihar ta Kano ya shigar ta hannun Barrister Sunusi Musa (SAN), gwamnatin tana bukatar kotun ta ayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ba shi da hurumin umartar CBN ya dakatar da amfani da takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000 - ba tare da tuntuba da amincewar majalisar gudanar da tattalin arziki da kuma majalisar magabata ta kasar ba.

A don haka ne gwamnatin jihar ta Kano take son kotun ta soke matakin babban bankin na Najeriya na janye takardun kudaden, saboda abin ta kira - wahalar da al'ummar jihar ke fuskanta a dalilin matakin bankin.

A tattaunawarsa da BBC, lauya Sunusi Musa, wanda shi ne ya shigar da karar, ya ce a ranar 15 ga watan Fabarairu kotun za ta saurari karar.

Harwayau gwamnatin tana son kotun ta bayar da umarnin da zai tilasta wa gwamnatin tarraya ta soke shirin nata na sauyin kudi saboda a cewarta ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar na 1999.

Kafin wannan, gwamnonin jihohin Kaduna da Zamfara da Kogi ma sun shigar da kara kan batun, har kotun kolin ta dakatar da CBN aiwatar da wa'adin da ya sa na daina amfani da takardun kudin na ranar 10 ga watan na Fabarairu har sai ta yanke hukunci a ranar 15 ga watan na Fabarairu na 2023.