Everton da Nottingham Forest ba su da tabbas kan makomarsu

Everton

Asalin hoton, BBC Sport

An wallafa

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Everton da Nottingham Forest ba za su iya sanin makomarsu ba har sai bayan kammala gasar Premier ta bana.

Everton na murnar rage hukuncin da aka yanke mata daga maki goma zuwa maki shida bayan ta ɗaukaka ƙara.

Amma duk da haka Everton da Forrest na da sabbin tuhume-tuhume da ake yi masu sakamakon keta dokokin hada-hadar kuɗi na gasar Premier League, inda za a gurfanar da ƙungiyoyin biyu a gaban wani kwamiti mai zaman kansa a farkon watan Maris, kuma dole ne su tabbatar da hukunci kafin ranar 8 ga Afrilu.

Idan har an yanke hukuncin cire maki, ƙungiyoyin biyu na da kwanaki bakwai domin ɗaukaka ƙara.

Dole ne a tabbatar da sakamakon wannan lamari kafin babban taron gasar Premier League wanda za a gudanar a ranar 24 ga watan Mayu, kwana biyar bayan an kammala kakar wasa ta bana.

Hakan na nufin cewa idan har ƙugiyoyin biyu sun fuskanci hukuncin cire maki suna iya samun kansu a matakin gasar 'Championship' ko da kuwa sun kai labari sakamakon wasannin da suka buga a kakar wasa ta bana.