Pogba ya kammala komawa Juventus

An wallafa

Paul Pogba ya kammala komawa Juventus, bayan da kwantiraginsa ya kare a Manchester United, kamar yadda kungiyar ta sanar ranar Litinin.

Mai shekara 29 dan kwallon tawagar Faransa ya koma Turin, bayan kaka shida a Old Trafford a matakin wanda bai da yarjejeniya da wata kungiyar.

Pogba ya koma United daga Juventus a 2016 kan fam miliyan 89 a matakin wanda aka saya mafi tsada a tamaula a duniya.

United ta kasa kulla yarjejeniya da Pogba, domin ya ci gaba da taka leda a Old Trafford, daga nan ta sanar cikin watan Yuni cewar dan wasan tawagar Faransa zai bar kungiyar.

Ana sa ran Pogba zai bi Juventus zuwa Amurka domin buga atisayen tunkarar kakar bana.

Juventus za ta buga wasan sada zumunta a Amurka da Barcelona ranar 27, sannan kwana uku tsakani ta fafata da Real Madrid.

Kaka biyu a jere, Juventus tana yin ta hudu a teburin gasar Serie A da tazarar maki 16 tsakaninda da AC Milan, wadda ta dauki kofin kakar da ta wuce.

Juventus ta ci karo da koma baya, bayan da ta lashe Serie A karo tara a jere, inda Pogba ya bayar da gudunmuwa a daukar kofin da ta yi tsakanin 2012-13 zuwa 2015-16.

Ya ci kwallo 34 a wasa 178 a Juventus, wadda ya koma taka leda a 2012, bayan da kwantiraginsa ya kare a Old Trafford a matasan kungiyar.

A kakar farko a Old Trafford, Pogba ya dauki League Cup da Europa League daga nan kuma ya fara fuskantar kalubale.