Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta taya Lewandowski
Barcelona ta taya dan kwallon tawagar Poland, mai taka leda a Bayern Munich, Robert Lewandowski.
Shugaban Barca, Joan Laporta ya ce yana fatan kungiyar Jamus din za ta amince da tayin da suka yi.
Dan wasan mai shekara 33, yana Bayern Munich da taka leda tun 2014, wanda a watan Mayu ya sanar cewar yana son gwada kwazonsa a wata kungiyar a bana.
''Mun taya dan wasan, muna jiran amsa, za mu gani ko cinikin zai tabbata,'' in ji Laporta kamar yadda ya sanar ranar Alhamis.
Saura kaka daya kwantiragin Lewandowski zai kare a Bayern Munich.
Laporta bai sanar da kan nawa ta taya dan kwallon ba, amma wasu rahotanni na cewar ta taya kan fam miliyan 33.8 da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan 4.2.
Lewandowski ya ci kwallo 238 a lik a wasa 252 a kaka takwas a Bayern da lashe Bundesliga takwas da Champions League.